Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RIGAR 'YANCI

Goma Sun Mutu A Karon Battar Zamfarawa Da ’Yan Bindiga

by Muhammad
January 21, 2021
in RIGAR 'YANCI
2 min read
Shanu
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Rabiu Ali Indabawa,

A kalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu bayan wani hari da ‘yan bindiga suka kai Jihar Zamfara. ‘Yan bindigar sun kai farmaki kauyen Talli, Dutsin Gari da Rayau a Kanoma dake Karamar Hukumar Maru, Sun kashe manyan shugabannin ‘yan kungiyar sa kai dake kauyakan, sannan sun kai farmaki gidaje da dama dake kauyakan, inda aka kiyasta a kalla mutum 10 sun rasa rayukansu da gidajensu a samakon wannan hari, babau shakka harin ya yi muni ta yadda suka mamaye kauyukan Talli, Dutsin Gari da Rayau dake Karamar Hukumar Maru a Jihar Zamfara, kamar dai yadda jaridar Daily trust ta ruwaito.

Mazauna garin sun sanar da manema labarai cewa wasu ‘yan bindiga sun je Dutsen Gari a baburansu da niyyar su yi garkuwa da mazauna garin, ba su san ‘yan kauyen suna da cikakken shirinsu ba. Take a nan aka fara musayar wuta tsakanin ‘yan bindigan da ‘yan kauyen wanda aka yi sa’o’i da dama ana dauki ba dadi da su.

Bayan ganin ba za su samu nasara ba ‘yan bindigan suka tsere daga kauyen.

‘Yan bindigan sun zarce kauyen Rayau, a can inda suka yi artabu da mazauna wurin. “Yan bindigan sun kashe manyan shugabannin ‘yan sa kai na kauyen, sannan sun tsere da dabbobi da dama. Basu tsaya a nan ba, sai da suka tattaba gidajen wadanda suka tsere saboda tsoron zuwansu kauyen,” Kamar yadda wani mazaunin yankin ya ce.

Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan yankin ba, Muhammad Shehu,har lokacin tattara wannan bayanai. Sai dai wani ganau ya shaida wa BBC cewa sun tsere cikin dazuka don tsoron kada ‘yan bindigar su harbe su. Amma sun kashe fiye da mutane 10.

A cewarsa, sun samu nasarar tattaro gawarwaki 7, amma sai sun shiga daji tukunna za su nemo sauran. Sannan sojoji sun je bayan harin, amma ba su yi komai a kai ba. Kwamishinan harkokin cikin gida da na tsaro na Jihar Zamfara, Abubakar Dauran, ya ce ya tura jami’an tsaro wurin da lamarin ya faru, yanzu haka yana jiran ji daga gare su ne.

SendShareTweetShare
Previous Post

Hadimar Gwamna Ta Yi Murabus Domin Da Tsira Da Aurenta

Next Post

Hankula Sun Tashi A Maiduguri Bayan Babbaka Sojan Da Ya Harbi Farar Hula Hudu

RelatedPosts

APC

APC Ta Lashe Zaben Cike Gurbin Dan Majalisa A Jigawa 

by Muhammad
15 hours ago
0

Daga Munkaila Abdullah, Hukumar zabe ta INEC ta bayyana Jam'iyya...

Masar

Ilimi: Jakadan Kasar Masar a Nijeriya Ya Yi Alkawarin Hada Hannu Da Gwamnatin Kano

by Muhammad
15 hours ago
0

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Jakadan Kasar Egypt a Nijeriya ya...

Suleja

Mun Gamsu Da Ayyukan Dan Majalisar Wakilai Na Suleja – Inijinya Kabiru

by Muhammad
15 hours ago
0

Daga Muhammad Awwal Umar, An bayyana cewar irin rawar da...

Next Post
Farar Hula

Hankula Sun Tashi A Maiduguri Bayan Babbaka Sojan Da Ya Harbi Farar Hula Hudu

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version