Gwamna Badaru Ya Taya Al’ummar Musulmin Jigawa Murnar Sallah Karama

Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya sahun miliyoyin al’ummar musulman duniya wajen gudanar da sallar idi bayan kammala azumin watan ramadana.

Gwamnan wadda ya gudanarda sallar idin a babban birnin jihar dake Dutse ya yi kira ga al’ummar musulmi da su cigaba da gudanar ayyukan alheri kamar yadda su ka saba yi cikin watan da ya gabata na ramadan.

Haka kuma ya bayyana al’ummar musulmai a matsayin ‘yan uwan juna, masu kaunar juna, hakuri, yafiya da tausayin junansu.

‎Sannan gwamnan ya kuma yi kira ga al’ummar musulmi da su yi amfani da wannan dama wajen yiwa kasa addu’r zaman lafiya, cigaba da habakar tattalin arziki.

Sannan daga karshe yayi fatan alheri tareda addu’ar yin bukukuwan sallah lafiya ga al’ummar jihar Jigawa, Naj‎eriya dama duniya baki daya.

Exit mobile version