Jam’iyyar APC reshen jihar Taraba ta yi yi kakkausar suka ga mulkin Gwamna Agbu Kefas, inda ta ce bayan shekaru biyu a ofis ya gaza cika alkawuran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe. Jam’iyyar ta ce rashin tasirin gwamnatin PDP zai sauƙaƙa wa APC kwace mulki a shekarar 2027 a jihar.
Da yake magana a Jalingo, Sakataren APC na jihar, Fidelis Francis, ya zargi Gwamna Kefas da rashin ƙaddamar da muhimman ayyukan raya ƙasa, ciki har da barin hanyar zuwa ƙaramar hukumar gwamnan a lalace bayan gadoji sun karye. Ya bayyana mulkin nasa a matsayin “wanda bai shirya ba kuma ba shi da wani tsari.”
Francis ya ƙara da cewa PDP tun daga 1999 ba ta da abin da zata nuna wa jama’a a matsayin na ci gaba, yana mai jaddada cewa gwamnatin Kefas kawai “fentin gine-ginen da aka yi tun da yake yi, tana iƙirarin ayyukanta ne.” Ya ce: “Gwamnan ya taimaka mana da kashi 80 cikin dari. Ya yi aikin da zai sauƙaƙa wa jam’iyyar adawa ta karɓo mulki saboda ba shi da komai da zai nuna.”
Ya buƙaci mambobin APC da su kwantar da hankali tare da haɗa kai domin shiryawa zaɓen 2027, yana mai tabbatar musu cewa jam’iyyar ta koyi darasi daga kura-kuran baya. “Mutanen Taraba ba su da hujjar sake zabar Gwamna Kefas,” in ji shi, yana mai cewa APC ta riga ta fara dabarun da za su kayar da PDP a zaɓen mai zuwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp