Gwamnan Gombe Ya Nada Yuguda Akanta Janar

Daga Khalid Idris Doya,

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya amince da nadin Aminu Umar Yuguda a matsayin mai rikon Babban Akanta na Jihar Gombe.

Shugaban ma’aikatan gwamnati na jihar, Alhaji Bappayo Yahaya wanda ya isar da amincewar Gwamnan a cikin wata wasika da ya sanyawa hannu, ya ce “Hakan ya dace da ikon da doka ta baiwa mai girma Gwamna, Muhammadu Inuwa Yahaya, a sashi na 208 (2c) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya (wadda aka yi kwaskwarima)”.

Ya bayyana cewa nadin na Yuguda na zuwa ne bisa karamci da aminci, da sadaukar da kai ga aiki tare da kwarewarsa a aikin gwamnati, yana mai bukatar sa da ya zama mai sauke nauyin da aka dora masa, yayin aiwatar da ayyukan sa a sabon matsayin.

Kakakin gwamnan Gombe, Ismaila Uba Misilli, ya bayyana cewar, an haifi Aminu Yuguda ne a ranar 21 ga watan Nuwamban 1974, “Ya samu digirin farko dana biyu a sashin ilimin sarrafa kudi wato Accounting daga Jami’ar Maiduguri, da digirin digirgir (PhD) daga Jami’ar Jos. Har ila yau, yana da shaidar kwarewar akantanci ta ACA, kuma mamba ne a kungiyar kwararrun Akantoci ta kasa, FCNA da dai sauransu.”

Kafin nadin nasa, Mukaddashin Akanta Janar din ya kasance Daraktan Baitulmali a Hedikwatar Baitulmalin, Gombe.

Wannan nadin, wanda ya biyo bayan ritayar tsohon Akanta Janar, Umar Babagoro, ya fara aiki ne nan take.

Exit mobile version