Gwamnan jihar Neja, Muhammad Umaru Bago, ya amince da nada mata har guda dari da talatin da daya (131) a matsayin hadimai na bangaren nade-naden siyasa daban-daban.
Kakakin gwamnan jihar, Boloji Ibrahim, ya shaida ta cikin wata sanarwa a jiya cewa, mata 41 daga cikin wadanda aka nadan sun samu kujerun ko’odinetoci ne, yayin da sauran mata 90 suka kasance manyan mataimakan na musamman a bangarori daban-daban wato (SSAs).
Da ya ke taya wadanda aka nada din murna, gwamnan ya bukacesu da su yi aiki tukuru da bada nasu gudunmawar wajen samun nasarar gwamnati mai ci.
Bago ya ce, nadin mata da yawa cikin gwamnatinsa wani mataki na cika alkawuran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe da ya ce zai yi tafiya da mata wajen bada nasu gudunmawarta domin gina cigaba mai ma’ana jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp