Connect with us

RAHOTANNI

Gwamnatin Bauchi Za Ta Kara Kotunan Shari’a  

Published

on

Gwamna Muhammad Abdullahi Abubakar ya bayyana aniyar gwamnatinsa na Karin manyan kotunan shiyya a jihar Bauchi domin sauKaKa yadda ake tafiyar da al’amuran shara’a.

A cewar gwamnan, Bangaren shara’a yana da matuKar muhimmanci ga tsarin shugaba mai cikakken iko.

Gwamnan, wanda yake jawabi a yayin da yake rantsar da sabon jojin babban kotu da aka naDa, Mai Shara’a Adamu Muhammad Kafin Madaki, ya ce gwamnatinsa ta bai wa Bangaren shara’a muhimmanci, yadda Bangaren yake sa ido a Bangaren zartarwa da kuma na yin dokoki, inda kuma kowane Bangare yake zame wa talaka dama ta Karshe.

“Shi ya sa ya zama wajibi mai shari’a ake so ya zama mutum mai matuKar mutunci kamar yadda ake tsammani a wurin shugaba nagari. Shi ya sa nake cike da farin cikin cewar, mutumin da aka rantsar yau yana da irin wannan kamala da ake buKata kuma masanin shari‘ar ne, kana ya yi aiki  a matsayin alkalin kotun majistiri da kuma babban magatakardar kotu”, kamar yadda ya ce.

Abubakar ya kuma ba da tabbacin cewar, gwamnatinsa za ta yi dukkan mai yiwuwa domin samar da kyakkyawan yanayi da Bangaren shara’a yake buKata domin kyautata jami’an shari’a ta yadda za su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Ya kuma buKaci ma’aikatan shari’a da su ci gaba da bin Ka’idojin aikinsu, da kuma marawa gwamnati baya domin inganta Bangaren shari’a a jihar ta Bauchi.

 

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: