Gwamnatin Jihar Kano Ta Haramta Amfani Da Babura A Dajika

Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya sha alwashin amfani da sabbin Sarakunan da aka kirkira a Jihar domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya. A cikin abubuwan da gwamnatin za ta mayar da hankali, akwai dubawa tare da inganta harkokin tsaro a fadin jihar bakidaya.

Haka zalika, Gwamnan ya shirya taron harkokin tsaron ne a matsayin karo na farko a Masarautar Karaye cikin Karamar Hukumar ta Karaye, inda dukkanin Shugabannin sassan harkokin tsaro na yankin suka halarci zaman.

Har ila yau, an gudanar da babban taron ne a cibiyar harkokin addinin Musulunci ta Karaye. Sannan taron ya gudana tare da Sarkin Karaye Alhaji Ibrahim Abubakar II, a matsayin uban taron. Kazalika, kafatanin Hakimai guda tara na yankin wannan Masarauta sun halarci taron tare da sauran Dagatai, Malamai da Shugabannin al’umma bakidaya.

Haka nan, Gwamna Ganduje ya bayyana wa al’umma cewa, a lokacin da suka kirkiro sabbin Masarautu, sun fada cewa sun yi hakan ne domin samar da kyakkyawan ci gaba a Jihar ta Kano.

Gwamnan ya ci gaba da cewa, “da yardar Allah harkar tsaronmu za ta kara inganta,  jama’a kuma za su wadata da harkokin kiwon lafiya, tsarin ilmi shi ma zai kara kyautatuwa da sauran makamantan su. Za a ci gaba da gudanar da taron wayar da kan al’umma domin inganta harkokin tsaro a kasa da kuma samar da hanyoyin bincike a kan duk wani yunkurin  aikata muggan laifuka,” in ji shi.

Gwamnan ya ci gaba da cewa, muna sa ne da abubuwan da ke faruwa a Zamfara, Katsina, Sakkwato da kuma Kaduna, abin da ko kadan ba ma fatan afkuwar sa a wannan jiha tamu ta Kano ko da da wasa. Kamar yadda muke samun labara, rashin abinci a wadannan jihohi sai kara karuwa yake sakamakon yadda Manoma suka kasa zuwa gonakin nasu,  wasu wuraren ma an kone gidajen nasu, wasu kuma sun rasa iyayen, ‘yan’uwa da sauran su, in ji gwamnan.

Kazalika, Jihar Kano ta yi iyaka da wasu jihohin da wannan al’amari ke faruwa da su, sannan a duk lokacin da aka kaiwa masu aikata ire-iren wadannan laifuka hari, aka fatattake su daga wadancan jihoji, damar da ta rage musu ita ce Kano, kamar yadda jami’an tsaro ke shaida mana.

Saboda haka, ya zama wajibi mu dauki matakan gaggawa don samar da ingantattun tsare-tsare domin fuskantar wannan kalubale tun kafin faruwarsa, in ji Ganduje

“Za mu ci gaba da hada hannu da Sarakunanmu na Gargajiya da sauran Hukumomin tsaro, saboda bukatar da muke da ita na tunkarar wannan babban al’amari. Muna kuma bukatar kara karfin hanyoyin hana faruwar matsalar rashin wannan tsaro. Wannan shi ne dalilin da ya sa muke ganin yana da muhimmancin gaske mu shigar  da Sarakuna a cikin harkar dumu-dumu,” a cewarsa.

Daga nan ne kuma, Gwamnan ya umarci dukkanin Hakimai da su ci gaba da gudanar da tarukansu na wata-wata domin nazarin halin da tsaro ke ciki a yankunnasu baki daya, sannan a cewar tasa za su ci gaba da yi wa Sarakunan nasu bayani a kan duk abin da ya shafi tsaron.

Haka suma Dagatai, dole ne su rika ganawa a duk karshen wata tare da sanar da Hakimansu halin da ake ciki. A lokaci guda su ma masu Unguwanni, dole ne su rika gudanar da irin wannan ganawa kuma su tabbatar da sanar da Dagatansu abinda ake ciki.

Har ila yau, Ganduje ya bukaci jama’a su ci gaba da lura da zirga-zirgar jama’a a wuraren zamansu a fadin Jihar Kano baki daya. Ya ce, dukkanin jami’an tsaronmu za su ci gaba da aiki hannu da hannu domin tabbatar da kyakkyawan yanayi ga al’ummar wannan jiha baki daya, in ji shi.

Da ya ke tsokaci a kan damuwar da ake da ita kan batun Dazukan da ke kewaye da Jihar Kano, Ganduje bayyana cewa, tuni shirye-shirye sun yi nisa na samar da kididdigar adadin mutunen da ke zaune a cikin Dazukan domin tabbatar da takamaiman wadanda ke kai-kawo a cikin Dazukan. Ya ce, tuni mu ka yi magana da Bankin ci gaban Musulunci da kuma Gwamnatin Tarayya domin samar da wuraren kiwo don amfanin makiyayanmu, in ji shi.

Gwamnan ya ci gaba da cewa, “mun haramta amfani da Babura a cikin Dazukan Jihar Kano, domin mun fahimci cewa masu aikata laifuka na amfani da Babura ne wajen aiwatar da munanan ayyukan nasu. Haramta amfani da Baburan, na wani dan lokaci ne, saboda haka muna kira ga al’ummar da ke  zaune a wadannan yankuna da cewa suyi hakuri da wannan hali musamman ganin dokar ta dan wani lokaci ce.

Bugu da kari, za a ci gaba da gudanar da irin wannan taro a kafatanin sauran Masarautun guda hudu na Jihar Kano, sannan dukkanin Sarakuna  biyar din za a gayyace su zuwa ofishin gwamna domin bayyana musu fatan da muke da shi na tunkarar matsalar tsaro a Jihar Kano.

Haka kuma ga dukkan alamu wannan taro, kwalliya ta biya kudin sabulu. Domin kuwa, dukkanin jami’an tsaro sun bayyana nasu bangaren, haka nan su ma Sarakunan Garagajiya. Abin da ya rage yanzu kawai shi ne, mu tashi tsaye tare da hada hannuwa domin tabbatar da aiwatar  da abubuwan da za su inganta harkokin tsaron jiharmu da kasa baki daya,” in ji shi.

A karshe, dukkanin Shugabannin sassan tsaron sun jinjinawa Gwamna Ganduje, bisa jajircewarsa wajen tabbatar da yaki da matsalar ta tsaro a fadin jihar baki daya.

Haka zalika, Shi ma a nasa jawabin Sarkin Karayen, ya jinjinawa Gwamna Ganduje bisa baiwa matsalar ta tsaron muhimmaci da ya yi. Sannan ya tabbatarwa da mai girma Gwamna cewa, a koda yaushe a shirye suke don shi dukkanin wata gudunmawa da kuma goyon bayan da yake bukata, tare da yin aiki tare domin inganta harka tsaron Jihar Kano da ma kasa baki daya, in ji Mai Martaba.

Exit mobile version