Daga Haruna Akarada,
A ci gaban da gwamnatoci ke kokarin kai wa al’ummarsu da suke mulka, wannan ne ya sa gwamnatin Jihar Kano karkashin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kafa wata ma’aikata ta sa hannun jari domin ci gaban Jihar Kano da ma baki masu shigowa jihar domin kasuwanci. Wannan sabuwar hukumar ita ce ta sa hannun jari karkashin Hajiya Hama Ali Aware, domin bunkasa kasuwanci. Wakilin LEADERSHIP A YAU, HARUNA AKARADA, ya sami ganawa da daya daga cikin jagororin wannan ma’aikata wato Ibrahim Usman Bala inda ya yi karin haske game da wannan ma’aikata da ma alfanunta da ma irin nasarar da ‘yan kasuwa da masu sa hannun jarin su za su amfana; ga dai yadda hirar ta kasance:
Mai karatu zai so ya ji da wa muke tattaunawa.
Shin wannan hukumar daman mutane basu santa ba, shin sabuwa za a ce kenan?
To wannan hukuma zamu iya cewa sabuwa ce ko muce ba sabuwa ba, domin za ta iya kai wa shekara shida ko bakwai da kafawa karkashin jagorancin Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ba don komai ba mai girma gwamna ya kafa wannan ma’aikata ba sai don matasan jihar kano ya zama suna da aikin yi ko baki masu shigowa nan Jihar Kano. Wanda za su dogara da nasu, kuma zai bunkasa tattalin arzikin Jihar Kano, wannan dalili ne ya sa aka kirkiri wannan hukumar. Kuma abin da ya sa zan ce sabuwa ce da can ba a santa ba sai bayan zuwan gwamna ya samar da ita. Abin da mu ke kira ga jama’a ba sai kana da katon guri ba a’a ka zoma mu ji meye harkokinka tukunna. Saboda haka idan ka zo to wannan hukumar za ta shiga harkokinka tare da kare maka dukiyarka yanda dukiyarka idan Allah ya so kasa Naira 100 za ta zama 150 ko 200 ba tare da ka sami wata matsala ba.
Wannan hukuma daga kafa ta zuwa yanzu yaya ayyukanta ke gudana?
Gaskiya daga kafa wannan hukumar kamfanoni da dama sun shigo an yi abubuwa da dama na bunkasa kasuwanci a Jihar Kano, kuma muna fatan nan gaba kadan idan Allah ya yarda idan mutane suka fahimci wannan hukuma gaskiya za su amfana kwarai da gaske.
Wannan hukumar aikinta yana da yawa amma aikinta na farko ta nemo mutane wanda suke son su sa jari a Jihar Kano musamman wanda suke kalubalantar rashin guri na sana’a ko na hannun jari ko baki wanda ba garinsu bane suna tsoran dukiyarsu kar a lalata. Babban aikin wannan hukumar ta je ta gayyatoka ta sanar da kai cewa duk abin da kake tsoro za a kare maka su. Misali idan kasa miliyan 100, a nan Jihar Kano to wannan hukumar za ta tabbatar cewa baka sami gibin komai ba, tana kula maka da su domin zuwanka mutum da jarinsa ka ga ai Jihar Kano za ta amfana da rage matasa wanda basu da aikin yi. Idan Allah ya sa wani ya zo ya gina katuwar ma’aikata ya sa jari, to wannan mu kuma shi ne babban ribarmu kuma, abu na biyu idan baka da fili, to mu za mu ba ka guri ka yi gini domin Jihar Kano ta ci gaba wannan shi ne.