Connect with us

RAHOTANNI

Gwamnatin Kano Ta Jaddada Aniyarta Ta Horar Da Matasa Sana’u Iri Daban Daban – Muhammad Garba

Published

on

Kwamishinan Ma’aikatar yada Labarai, al’adu, Matasa da wasanni na Jihar Malam Muhammad Garba ya bayyana cewa Gwamnatin Kano Ta Jaddada Aniyarta Ta Horar Da Matasa Sana’u Iri Daban Daban. Kwamishinan ya yi

wannan bayani ne a lokacin da ya ke karbar bakuncin kungiyar wadanda suka koyi aikin gyaran Mota irin na zamani su 150 wadanda gwamnatin Kano ta dauki nauyin koyon aikin gyaran motoci kirar Peugeot lokacin

da suka kai masa ziyara a ofisihinsa.

Malam Muhammad Garba yace wadanda suka amfana  wanda kuma tuni suka kammala koyon aikin na tsawon shekara guda, yace Gwamnatin Khadimul Islam ta samar masu da kayan aiki tare da basu tallafin Naira dubu Hamsin (50,000.00) a matsayin jarin fara gudanar da harkokin sana’ar tasu Kwamishinan ya ci gaba da cewa daga cikin wadanan mutane 50 daga cikin jimlar wadanda suka samu irin wannan horo mata ne, an yi haka ne domin tabbatar da cewa ana tafiya da kowa da kowa acikin shirin wannan Gwamnatin na inganta sana’u a Jihar Kano Hakazalika Malam Muhammad Garba ya kara da cewa shirye shirye sun kammala na sake tura matasa 200 wadanda ake sa rana zasu kara samun horo a fannoni daban daban a kamfanin hada motocin Peugeot. Kason farko na mutane 72 na wadanda suka amfana tuni an yaye su kuma sun ci gaba da dogaro da kansu.

Tunda farko da yake gabatar jawabinsa shugaban Kungiyar Makanikan Ganduje Isma’ila Ibrahim ya jinjinawa Gwamna Dakta Abdullahi Umar Gamduje bisa kyakkyawan hangen nesan sa bisa kirkiro da ayyukanyi ga matasan Jihar Kano.

Da yake tofa albarkacin bakinsa a lokacin ziyarar makanikan Ganduje, mashawarci na musamman ga Gwamna Ganduje kan harkokin gyare gyare Injiniya Idris Hassan yace shirin samar da ayyukan yi ga matasa an

samar dashi ne domin inganta rayuwar matasan Jihar Kano. Kamar yadda kakakin ma’aikatar yada labarai na Jihar Kano Sani Abba Yola ya shaidawa Jaridar Leadership ayau Juma’a.

 
Advertisement

labarai