Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana shirye-shiryenta na tsarawa da kuma inganta harkar maganin gargajiya a jihar. Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da kwamitin rigakafi a jihar Kano.
Ya jaddada muhimmancin da masu aikin maganin gargajiya ke da shi a É“angaren kiwon lafiyar al’umma, tare da buÆ™atar haÉ—a kai tsakanin magungunan gargajiya da na zamani.
- Tinubu Ya Sake Nada Farfesa Sheshe Shugaban Asibitin Koyarwa Na Aminu Kano
- Mutane 4 Sun Mutu, 6 Sun Bace Sakamakon Kifewar Kwale-kwale A Kano
Gwamna Yusuf ya sanar da wasu tsare-tsare da za su tallafa wa masu sayar da magungunan gargajiya ta hanyar shirye-shiryen bayar da horo, da haÉ—in gwuiwa da cibiyoyin kiwon lafiya, da kuma kafa hukumar kula da masu sana’ar. WaÉ—annan matakan na da nufin kara inganta tsaron lafiyar jama’a, tabbatar da inganci, da kuma haÉ—a harkar magungunan gargajiya da tsarin kiwon lafiyar zamani a Jihar Kano.
Shugaban ƙungiyar masu maganin gargajiya ta ƙasa, Dr. Shaba Maikudi, ya jinjinawa gwamnatin bisa wannan tallafi. Ya yaba wa gwamna kan kulawa ta musamman ga masu maganin gargajiya da kuma farfaɗo da ɓangaren kiwon lafiya.
Dr. Maikudi ya yi kira ga gwamnati da ta kafa hukumar maganin gargajiya domin ƙara inganta harkar da tabbatar da haɗewar gargajiya a cikin tsarin kiwon lafiyar jihar.