Gwamnatin Nasarawa Ta Kafa Kwamitin Da Zai Binciki Ayyukan ’Yan Sandan SARS

Daraktoci

Daga Zubairu M Lawal, Lafia

 

A ranar Littinin, gwamnatin jihar Nasarawa ta kaddamar da kwamitin mutane bakwai da za su binciki ayyukan ‘yan sandan SARS da kuma musabbabin abin da ke hada tsakanin su da matasa.

Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullah Sule, ya yi kira ga kwamitin da su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya da rikon amana.

Duk wanda aka samu da laifin cin zarafin jama’a za a hukunta shi.

Gwamna Abdullah Sule, ya ce a jihar Nasarawa matasa sun nuna halin dattako da natsuwa saboda ba su fito tituna suna zanga-zanga ba, kuma babu wani abu makamancin wannan a jihar Nasarawa.

Hakan ya sanya gwamnatin jihar ta jinjina wa matasan jihar. Kuma ta kafa kwamitin da zai binciki tsakanin jami’an tsaro na SARS da kuma matasa.

Gwamnan ya yi kira ga al’umman jihar Nasarawa da su kwantar da hankalinsu, duk wanda yake da wani korafi kan cin zarafin da hukumar ta yi masa, to ya je gaban kwamitin ya bayyana masu, gwamnati za ta bai wa kowa hakkinsa.

Da yake bayyani ga manema labarai jim kadan bayan rantsar da kwamitin, Shugaban kwamitin mai shari’a Badamasi Maina (ritsya),  ya tabbatar da cewa kwamitin zai yi aiki tsakaninsa da Allah, kuma kwamitin zai ji ba’asin kowane bangare, ba wai zai zauna waje daya ba ne ko kuma ya hada rahoto ya kawo wa gwamnati ba.

Ya ce kowa ya kawo korafin shi duk wanda hukumar SARS ta yi masa ba dai dai ba cikin kananan hukumomi 13 da ke karkashin kwamitin,  in dai a jihar Nasarawa ne mutum yake idan hukumar SARS sun taba cin zarafinsa to ya kawo koke da hujja zuwa gaban kwamitin kofarsa a bude take tun daga yau.

Shi ma Shu’aibu Sani, shugaban Matasa ya ce, wannan kwamitin zai bai wa matasa damar su fito su bayyana damuwarsu game da aika-aikar da hukumar SARS ta yi mu su na muzgunawa.

Kuma duk wanda zai zo ya tabbatar yana da hujjojin da za su gamsar da kwamitin saboda da wannan hujjar ce  za a yi amfani wajen hukunta duk wanda aka samu da laifi.

Ya ce, gwamnati ta yi hikima wajen kafa wannan kwamitin, saboda ya zo a daidai domin yanzu a kasar nan jihohi da dama suna gudanar da zanga-zanga. Amma a jihar Nasarawa babu wannan.

Shi ma Sakataren Jam’iyyar APC ta Jihar Nasarawa, Alhaji Aliyu Bello, ya yaba wa Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullah Sule,   wajen samar da wannan kwamitin da zai duba ko akwai zargin cin zarafin da hukumar SARS ta yi wa wani a jihar, saboda a magance matsalar.

Ya ce, cin zarafi ba shi da dadi hakan ya sanya matasa suka dukufa zanga-zanga a wasu jihohin kasan nan saboda cin zarafin da SARS suka yi ba shi da dadi.

Alhaji Aliyu Bello, ya kara da cewa, a zanga-zangar da ake yi wasu matasan su na yi ne tsakaninsu da Allah, saboda a kawo karshen cin zarafin da ‘yan sandan SARS ke yi.

Amma wasu matasan ana amfani da su ne domin lalata gwamnati, bai kamata matasa su bari ana amfani da su ba, saboda su ne manyan gobe, nan gaba kadan kasar nan za ta koma a hannunsu.

Exit mobile version