Gwamnatin tarayya ta fitar da sabon tsari wajen canza layin wayar salula ga kamfanonin sadarwa a Nijeriya. Ta bayyana cewa, ta fitar da wannan sabon tsarin ne domin tabbatar da ganin an hade kowani da yi da katin lambar dan kasa. Ta kara da cewa, za ta yi aiki kafada da kafada da dukkanin masu ruwa da tsaki da ke cikin kamfanonin sadarwa wajen tabbatar da ganin an yi aiki da wannan sabon tsarin.
Sabon tsari a kan canza layin wanda ministan sadarwa da tattalin arzikin kimiyya, Isa Pantami ya amince da shi, an samar da shi ne ga wadanda layukansu ya bace ko ya lalace ko aka sace.
Gwamnatin tarayya da bayyana wannan ne a wani takarda da jami’in hudda da jama’a na hukumar sadarwa, Ikechukwu Adinde da babban jami’in sadarwa a hukumar kula da katin dan kasa, Kayode Adegoke suka rattaba hannu. gwamanatin tarayya ta bayayana cewa, yanayin yadda za a dunga canza layukan dai shi ne, dole ne sai wanda zai canza layi ya nuna lambar katin zama dankasa kafin a canza masa layi. Wannan yana daga cikin ka’idojin hukumar sadarwa ta kasa ta gindaya na saka sabon layi.
A ranar 15 ga watan Disambar shekarar 2020, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa dole ne kowani layin waya a hade shi da katin lambar dan kasa kafin ranar 30 ga watan Disambar shekarar 2020, inda ta umurci kamfanonin sadarwa su rufe duk wani layin waya da ba a hade da lambar dan kasa ba idan wa’adin ya wuce. Amma daga baya an kara tsawan makwanni uku sakamakon an gudanar da sanarwar da wuri, inda aka ka ihi zuwa ranar 19 ga watan Junairun shekarar 2021. Daga baya kuma an kara wa’adin mako shida wanda ya sa aka kai shi zuwa ranar 9 ga watan Fabrairun shekarar 2021.
“Kwamitin zai saka ido ne wajen tabbar da an hade layukan waya da lambar katin dan kasa .”
Ta kara da cewa, bisa amincewar wannan kwamiti ne ya bayar da damar aiwatar da wannan sabon tsari a kan canza layin wayar salula. Ta ce, an aiwatar da tsarin ne domin ya bai wa kamfanonin sadarwa gane wanda ke bukatar canza layin waya, ga mutanen da layin su ya lalace ko aka sace ko ya bace, wanda cikin sauki kamfanonin sadarwar za su canza layin.