Daga Rabiu Ali Indabawa,
Gwamnatin Tarayya ta karyata rade-radin da yadawa na cewa ta biya kudin fansar karbo daliban Kwalijin Kagara dake Jihar Neja. A cewarta ba ta biya ba, ba kuma za ta biya kudin fansa ba domin karbo daliban da Malaman Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara a Jihar Neja da’ yan bindiga suka sace ba.
Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, shi ya fadi hakan a gidan talabijin na Channels TB mai suna ‘Sunrise Daily’ a ranar Asabar dangane da jita-jitar da ke yaduwa, cewa an saki wadanda aka sace bayan Gwamnatin Tarayya ta biya Naira miliyan 800.
Game da abin da Gwamnatin Tarayya ke yi dangane da lamarin, Lai Mohammed ya ce: “Na kasance a Minna tare da abokan aiki na, Ministocin Cikin Gida da Harkokin’ Yan sanda, IG, da Mashawarcin Tsaron Kasa, a ranar Laraba, don samun bayanai kai tsaye game da sace wadannan yaran makarantar Kagara.