Gwamnatin tarayya ta sake jaddada aniyar ta na aiwatar da wani shirin na musamman da zai bayar da damar samar da hanya daya tilo na tattara kudaɗen haraji mai suna ‘National Single Window (NSW),’ wani hadaɗɗiyar manhaja na sauƙaƙa harkokin kasuwanci da nufin toshe sulalewar kudaɗen shiga, da kyautata gaskiya, da ingantattun hanyoyin kasuwanci na ƙasa da ƙasa.
da yake jawabi a lokacin da ya bayyana a gaban hadakar kwamitin harkokin Kwastam a ƙarƙashin jagorancin Sanata Senator Isah Jibrin, ministan kuɗi da tsare-tsaren tattalin arziki, Mista Wale Edun, ya bayyana muhimmancin da hukumar Kwastam ke da shi kan tattali arziki ƙasa.
“Harajin da Kwastam ke tarawa har yanzu shi ne babba wajen samar wa asusun gwamnatin tarayya kuɗin shiga wanda ke amfanar da ita kanta gwamantin tarayya da jihohi,” Edun ya shaida.
- Matsayar Bai Daya Da Sin Da Amurka Suka Cimma Ta Fuskar Haraji Na Da Babbar Ma’ana
- China Ta Mayar Da Martani Kan Barazanar Trump Na Ƙarin Haraji Ga Kasashen BRICS
Ya ƙara da cewa, “Muna aiki tuƙuru domin ƙara kyautata hanyoyin tara kudaɗen shiga da toshe ƙofofin sulalewar kudaɗen shiga.”
Ministan ya bayyana cewa gwamnatin Shugaban ƙasa Bola Tinubu ta ci gaba da mayar da hankali wajen gyara rugujewar tsarin da tattalin arzikin ƙasar nan, musamman biyo bayan cire tallafin man fetur da kuma sauya tsarin musayar kudaɗen waje na kasuwa.
“daidaita farashin ya kasance hanya daya tilo da za a iya amfani da ita wajen tafiyar da harkokin kasuwa da kuma tabbatar da gaskiya,” in ji shi.
Edun ya nuna ƙalubale a tsarin biyan ciniki a Nijeriya, tare da lura da cewa har yanzu ana samun yawan hada-hadar kasuwanci ta hanyoyin da ba kamata ba.
Ya bayyana cewa gwamnati na binciken gyare-gyare da nufin ƙara bayyana gaskiya, ciki har da yiwuwar gudanar da cinikin danyen mai daga ƙasashen waje da na naira.
“Yawancin mu’amalar kasuwancinmu ana gudanar da su ne a waje da tashoshi na yau da kullun. Muna aiki kan gyare-gyaren da za su inganta tsarin,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp