Gwamnatin Tarayya ta shirya tsaf, domin kafa cibiyar kula da hakar ma’adanai ta kasa wadda kuma za ta kasance ta cika bukatun masu son zuba jari a fannin.
Dakta Mary Ogbe, babbar sakatariya a ma’aikatar bunkasa ma’adanai da karafa ta sanar da hakan a makon da ya wuce a yayin kaddamar da ‘ya’yan kwamtin wanda aka gudanar a shalkwatar ma’aikatar da oe Abuja.
Kazalika, a cikin sanarwar da Mataimakin Daraktan samar da bayanai na ma’aikatar Alaba Balogun ya fitar ya ce,cibiyar za ta taimaka wajen kokarin da ake yi na farafado da fannin ma’adanai da kuma yin kokari wajen ganin fannin, ya taimaka don a kara habaka tattalin arzikin kasar.
Dakta Mary Ogbe ta ce, akwai mahimmanci da dama na kafa cibiyar na domin cimma burin ma’aikatar kan bunkasa tattalin arzikin kasar nan, musamman ta hanyar yin hadaka da manyan sassan ofis-ofis na ma’aikatar.
Ta bayyana cewa, an kafa cibiyar ne domin a cimma bukatun masu zuba jari a fannin tattalin arziki.
Ta kuma nuna jin dadinta wajen cimma burin nauyin da aka dorawa ‘ya’yan cibiyar ta hanyar yin hadaka ta kasa da kasa da kuma yin hadin guiwa da masu zuba jari a fannin.
Ta kara da ministan kula da ma’adanai Dakta Dele Alake, ya bayar da tabbacin cewa, a shirye yake don ya bai wa cibiyar goyon bayan da ya dace don ta sauke nauyin da aka dora mata.
A cewarta, cibiyar za ta yi hadaka da manyan sassa na ma’aikatar.
‘Ya’yan kwamitin an zabo su ne daga sassa da ban da ban na ma’aikatar wanda kuma Daraktan sashen zuba jari na ma’aikatar zai jagoranci kwamitin.