Kamfanin ARCO ya shafe fiye da shekaru 35 yana aiki bisa ƙwarewa da nuna juriya a ɓangaren kula da gyare-gyare a masana’antar mai da iskar gas. ARCOS Kamfani ne ɗan kasa (Nijeriya), da ya nuna karansa ya kai tsaiko da zai iya shigewa gaba wajen jagorantar Nijeriya a masana’antar mai da iskar gas, don haka ya cancanci samun lambar yabo ta Leadership ta gwarzon kamfani ɗan ƙasa a masana’antar Mai da iskar Gas na shekara ta 2024.
ARCO Group Plc. yana ɗaya daga cikin manyan kamfanonin kula da harkokin injinan samar da man fetur da iskar gas a Nijeriya da ya samu ci gaba mai yawa a sakamakon manufofin cikin gida na kasar. Samar da waɗannan manufofin na cikin gida, ya ba ARCO damar ɗaukaka fiye da yadda yake a masana’antarsa ta farko, inda ya haɗe ayyukansa zuwa rukunin kamfanoni masu ƙarfi na duniya. A ranar 1 ga Afrilu, 2015, waɗannan kamfanoni suka haɗe zuwa rukuni a ƙarƙashin sunan, ARCO Group.
- Jerin ‘Yan Wasa Uku Da Suka Zura Kwallaye 100 A Gasar Zakarun Turai
- Ɗansanda Ya Gamu Da Ajalinsa Bayan Fasa Tukunyar Miya A Adamawa
ARCO Maintenance and Engineering Limited (AMEL), wanda a baya aka fi sani da ‘ARCO Petrochemical Engineering Company’ yana da ƙwarewa sosai a ɓangaren kulawa da gyare-gyare na manyan injina da kayan aikin gas da suka haɗa da (gas turbines, turbines da compressors) da kuma bangaren samarwa tare da kula da wutar lantarki. Yana da ƙwararrun ma’aikata ‘yan Nijeriya, fiye da 170, waɗanda ke samun horo daga abokan hulɗa na fasaha na duniya a yayin taron ƙara wa juna sani.
Dalilan da suka sanya ARCO ya zama zakaran gwajin dafi a cikin gida shi ne, a shekarar 2007, yayin da rashin kwanciyar hankali ya yi ƙamari a yankin Neja-Delta, manyan kamfanoni na duniya da ke kula da injina da kayayyakin aikin iskar gas, dole ta sanya suka kwashe Injiniyoyin su suka fice daga yankin. Bayan ficewarsu sai alhakin kula da nagartar kayan aiki ya hau kan injiniyoyin ARCO.
ARCO, take ya yi damara ya tura matasa ‘yan Nijeriya da ya horar domin ci gaba da gudanar da aikin da Injiniyoyin ƙasashen waje suka fice suka bar wa kamfanin. Wannan babban abin mamaki ne ga masana’antar.
Kazalika a lokacin rashin kwanciyar hankali a yankin Neja-Delta, ma’aikatan jirgin ruwa na Nijeriya waɗanda suka ƙware kamar takwarorinsu na ƙasashen waje, bayan ficewar takwarorinsu na ƙasashen waje, dole aka kira na cikin gida suka ci gaba da gudanar da ayyukan kula da sarrafa jiragen kamar yadda takwarorinsu da suka fice ke yi ko fiye da haka.
A yau, Nijeriya ta samu sauki wajen kashe kuɗaɗen gudanarwar ayyukan jiragen ruwanta da fiye da kashi 40 cikin 100 saboda masu aikin ‘yan asalin ƙasar ne, waɗanda ARCO ya taimaka wajen gina hikimarsu da basirarsu, yanzu suna taka rawa sosai wajen sarrafa kayayyaki da injina a ɓangaren ruwa da teku.
Rukunin ARCO ya sama wa kansa gurbi a fannin mai da iskar gas a Nijeriya, inda ya mai da hankali kan dabarun sarrafa kayayyakin ruwa da kulawa da gwajin fasahar jirage marasa matuƙa.
Yau kimanin shekaru 38 da kafa wannan kamfani, Rukunin ARCO yana jan ragama a masana’antar mai da iskar gas, wanda ya kuduri aniyar cimma burinsa na kai wa kamfani mai juya hannun jarin biliyoyin daloli zuwa 2025.
Okoigun, shi ne Manajin Darakta na rukunin ARCO a yanzu. ARCO na tallafa wa matasa ‘yan kasuwa ta hanyar ɗaukar nauyin taron ƙarawa juna sani da bayar da tallafin karatu ga matasa ɗaliban injiniya, wanda ya samu lambobin yabo da dama saboda gudunmawar da ya bayar a ɓangaren man fetur da iskar gas na ƙasa.
ARCO ya fi mayar da hankali kan ayyukan mai da iskar gas tun kafin a sarrafa su. Rukunin ARCO ya kasu kashi huɗu da suka haɗa da:
- ARCO Marine, yana kula da ɓangaren ruwa na masana’antar mai da iskar gas.
- ARCO Maintenance and Engineering, yana kula da gyare-gyaren kayan aiki na mai da iskar gas
- ARCO Integrity, yana kula da ɓangaren gwaji don tabbatar da nagartar kayayyaki.
- ARCO worldwide, ya mayar da hankali kan masana’antar jirage marasa matuka.
A yayin da rukunin ya fara shahara, ya fitar da sanarwar ɗaukar ma’aikata kimanin 500. Wannan ci gaba ya biyo bayan wasu sauye-sauye da yawa da rukunin ya yi wanda ya kai shi ga wannan nasarar, kamar zaɓar mutane don yin amfani da su a tsarin tattalin arziƙi mai nagarta.
A nan gaba, rukunin yana da burin fara fitar da kayayyakin ARCO zuwa sauran ƙasashen duniya. Wasu daga cikin ɓangarorin da Rukunin ARCO da ake tunanin shigo da su don ƙara faɗaɗa kamfanin sun haɗa da fannin fasaha da noma da jirage marasa matuka da kuma kafofin yaɗa labarai, domin yana son yake kallon kansa a matsayin wani kamfani na Nijeriya a duniya.
Duba da irin waɗannan nasarorin, ya sa ARCO ya zama gwarzon kamfanin ƙasa a masana’antar mai da iskar gas da ya cancanci samun lambar yabo ta kamfanin LEADERSHIP ta bana.