Mukaddashin shugaban Nijeriya, Yemi Osinbajo, ya ce gwamnatin Kasar za ta fara daukar amfani da kalaman nuna kiyayya a matsayin ta’addanci, kuma ya ce gwamnati ta ja layi a kan batun daga yanzu.
Osinbajo, ya bayyana haka ne a lokacin taron Kwamitin Kula da Tattalin Arziki na kasa, wanda ake gudanarwa a ranar Alhamis a fadar shugaban kasa da ke Abuja.