Karshen shekara lokaci ne na waiwaye adon tafiya. Sai dai a wannan shekarar da muke ciki, mun gane ma idanunmu dimbin abubuwan takaici da suka abku a duniya. Wani abu da zai iya sanyaya zuciyarmu shi ne, yadda huldar hadin gwiwa ta Sin da Afirka ke bunkasa yadda ake bukata. Kamar dai yadda shugaba Bola Tinubu na kasar Najeriya ya fada, a taron kolin dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) da ya gudana a birnin Beijing na kasar Sin a bana, cewa ”yayin da ake fuskantar kalubalolin tattalin arziki da na siyasa dake addabar duniya, huldar Afirka da Sin ta nuna yanayi na jajircewa, ta yadda ta zama wani abin koyi ga kasa da kasa.”
Dangane da jajircewar da shugaba Tinubu ya ambata, za a samu cikakken bayani ne cikin jawabin da mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, ya yi a jiya Talata, kan ayyukan da aka yi a kasar Sin a fannin diplomasiyya cikin shekarar 2024. A cikin jawabin, Wang ya ambaci sakamakon taron koli na dandalin FOCAC da ya gudana a Beijing a wannan karo, yana cewa, ”Shugabannin Sin da Afirka sun cimma ra’ayi daya, kan gina al’ummar Sin da Afirka mai kyakkyawar makomar bai daya ta sabon zamani, dake iya jure duk wani yanayi.” To, maganar ”jure duk wani yanayi” da ”jajircewa” suna da ma’ana kusan iri daya. Wato duk wani kalubale da ake fuskanta, kuma duk wata matsalar da ake fama da ita, Sin da Afirka za su yi kokarin neman ci gaba na bai daya, kafada da kafada.
- Tattalin Arzikin Kasar Sin A Matsayin Bango Majinginar Duniya
- Dangote Ya Musanta Labarin Ciyo Bashin NNPC Na Dala Biliyan 1 Domin Tallafa Wa Matatarsa
To, sai dai ta yaya ake aiwatar da matsayar da aka cimma? Wang ya ambaci wasu matakan tallafawa kokarin raya kasa guda 8, da Sin take gudanar da su a hadin gwiwarta da dimbin kasashen dake nahiyar Afirka, wadanda suka shafi rage talauci, da samar da isasshen abincin da ake bukata, da kirkiro sabbin fasahohi, da dai sauransu. Kana jami’in ya ambaci yadda kasar Sin ta cire kudin kwastan kan kayayyakin da take shigowa daga kasashen da suka fi fama da rashin ci gaba da suka kulla huldar diplomasiyya da ita, da aikin hadin kai da Sin da Afirka ke gudanarwa, mai nasaba da fannoni 10 da suka hada da ciniki da zuba jari, da tsarin samar da kayayyaki, da dai makamantansu.
Sai dai don tabbatar da jajircewar huldar hadin kai tsakanin Sin da Afirka, ban da ingantattun manufofin da ake aiwatar da su a halin yanzu, ana bukatar samun hasashe mai yakini kan makomar huldar. Dangane da wannan fanni, za mu iya duba jawaban da aka yi wajen muhawarar Mjadala Afrika, da ta gudana a kasar Habasha a kwanakin nan. An yi muhawarar ne tsakanin mutane masu takarar neman kujerar shugaban majalissar kungiyar kasashen Afirka ta AU, inda aka ba mutanen da za su iya zama shugaban majalissar kungiyar AU damar bayyana manufofin raya nahiyar Afirka da za su iya dauka a nan gaba, idan sun ci nasarar lashe zaben.
Sai dai a bisa ra’ayin ‘yan takara na kasashen Kenya, da Djibouti, da Madagascar, da dai sauransu, makoma mai haske ta nahiyar Afirka ta dogara kan karfafa huldar abota, da za ta tabbatar da kirkire-kirkire, da adalci, da samun ci gaba tare, inda kasar Sin za ta taka rawar gani a ciki.
Abun lura shi ne, burikan da wadannan ‘yan siyasa suka ambata a jawabansu, irinsu kokarin gina yankin ciniki cikin ‘yanci na Afirka, da karfafa ciniki tsakanin kasashen Afirka, da amfani da tsarin fasahar dijital wajen sa ido kan yadda ake aiwatar da Ajandar 2063, da inganta kwarewar kasashen Afirka a fannonin tinkarar bazuwar annoba da ke abkuwa ba zato ba tsammani, da nemo kayayyakin aikin jinya da ake bukata, sun dace da matakan hadin gwiwar da ake yi tsakanin Sin da Afirka, da ta shafi aiwatar da shawarar ”Ziri Daya da Hanya Daya”, da yada fasahohin dijital zuwa karin wurare, da aikin jinya, da dai makamantansu. To, wadannan abubuwa sun shaida cewa, akwai tabbaci ga huldar hadin kai ta Sin da Afirka, cikin wani dogon lokaci mai zuwa.
Cikin jawabinsa ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce kasar Sin za ta yi amfani da yanayin tabbas da take da shi wajen tinkarar yanayin rashin tabbaci da ake fama da shi a duniya. To, a ganina, jajircewar huldar hadin kai tsakani Sin da Afirka ita ma tana samar da tabbaci, da imani, da kwanciyar hankali ga duniyarmu, da ke fama da yanayin tangal-tangal a halin da muke ciki. (Bello Wang)