Kwamishinan ayyuka na jihar Kano Injiniya Ma’azu Magaji ya bayyana cewa hakkin gudanar da managartan ayyuka da zasu ciyarsa kasarnan gaba a fannin kere-kere da gine-gine ya ratayane akan Injiniyoyi.
Kwamishinan wanda ya bayyana hakan a yayin gudanar da taron tsofaffin daliban tsangayar koyar da Injiniya ta jami’ar Bayero da aka yi daya daga cikin dakunan taro na jami’ar a ranar Asabar.
Injiniya Ma’azu Magaji Dan sarauniya ya ce, wajibi ne Gwamnatoci a kowane mataki a kasar nan su kara kokari wajen bunkasa karatun aikin injiniya yanda ya kamata da za su kasance suna gudanar da ayyukan kere-kere a kasar nan ba tare da la’akari da dogaro dana kasashen waje ba.
Ya yi nuni da cewa a matsayinsu na kwararru da suka sami horo za su zauna su gayawa kansu cewa yakamata su tsaya su tabbatar da cewa duk inda suka sami kansu ba za a yi amfani dasu wajen gurgunta rayuwar kasar nan ba da kuma ayyukan da ake ba.
Ma’azu ya ce, hakan zai kawo cigaba sosai mai amfanarwa ga kasa da al’ummarta dasu kansu injiniyoyi