Hakuri Ne Jigon Samun Nasarata –Dahiru Abubakar 

Manajan motocin sufuri na Gwamnatin Jihar Adamawa reshen Mararraba Abuja, Alhaji Dahiru Abubakar Tula, ya bayyana makasudin samun nasarar da ya yi a aikinsa inda ya ce, hakuri ne jigon samun nasararsa. dahiru Tula ya bayya hakan a wata tattaunawa da wakilin LEADERSHIP A YAU RABIU ALI INDABAWA, jim kadan bayan karbar lambar yabo da jaridama suna, WATA SHARI’A SAI A LAHIRA ta yi a Mararraba dake Abuja, ga yadda ta kasance.

Da fari za mu so sanin sunanka da tarihinka a takaice

Alhamdulillahi, ni haifi dahiru Abubakar a garin Tola dake yankin karamae Hukumar Mayo Belwa Jihar Adamawa, na yi karatun firamare a Tola 1 Primary School, sannan na wuce zuwa makarantar gwamnati ta jeka ka dawo a Tola da sauran ilimai na zamani da na addini a can. Daga nan ne na fara aiki da Kamfanin sufurin motoci na gwamnati Jihar Adamawa, na zauna a Area 1 Abuja a farkon mulikin Tsohon Shugaban kasa Obasanjo bayan an yi mana rusau muka koma Mararraba, wannan har yanzu muna Mararraba.

An kai ni Kaduna na yi aiki, sannan an kai ni Mombila, aka sake dawo da ni Kaduna na rike manaja, sannan na rike Tashar motocin ta Jabi da ke Abuja a matsayin Manaja. Sannan na rike manajan tashar mota ta Mombila.

An ce in je in zauna a can kafi a kawo min motoci, daga baya na yi korafi cewa tun da babu motoci gara na je na yi aiki a wani wuri da na sani, to sai aka mayar da ni Kaduna, daga aka sake dawo da ni tashar Maraba, a halin yanzu ina nan Mararraba a matsayin manaja karkashin kamfanin sufurin motoci na Jihar Adamawa.

To ranka ya dade ko za ka iya gaya mana irin gwagwarmayar da sha tsakaninka da abokan aikinka?

To ka san aiki a zamanin nan abubuwa sun canja fiye da yadda kake tsammani. Gaskiya na sha gwarwarmaya ba ma da abokan ba har ma da kamfaninmu, na samu matsaloli da yawa. Matsala ta farko ita ce, rashin tabbatar da ni a matsayina na manaja sai da shafe wajen shekara 13 ko 14 ina ta gwagwarmaya. To sannan kuma ka san shi yanayin in kana aiki da mutane dole ne kana hada wa da hakuri, domin hakuri ya fi komai, domin wani ma kana ji zai ce ba ya kaunarka, har muka zo lokacin da aka ba ni Shugaba na motocin bas na gwamnati na reshen Abuja, lokacin ma bana nan ina Yola ne, mutane suka zauna suka suka ce kai zamanmu hakan nan bai cancanta ba yakamata a ce muna da shugaba.

To a cikin mu manajoji muna Kamfanin Jihar Adamawa lokacin ina karkashin wani ne, akwai Kamfanin Jihar Bauchi, akwai Kamfanin Jihar Yobe, akawi Kamfanin Jihar Borno, sannan kuma akwa Kamfanin motocin Jihar Katsina, akwai kuma wadanda suke makale da mu. Su suka zauna suka ce wanda ya cancanta ya yi musu shugabanci nine.

Ina zaune a Yola da suka gama tattaunawa sai suka kira ni suka ce, mu fa mun zauna mun tattauna kuma mun zabe ka a matsayin shugaba, tun da a da can ma akwai abubuwa da suka duba da suka hada iya mu’amala da mutane da suka ga ina yi, sannan duk wani abu da ya damu dan kungiya za su ga ni ma ya dame ni ko da kuwa ba daga bangarena yake ba. Direban Bauchi ko Gombe ko na wani wuri idan wani abu ya same shi kamar tsautsayi na zuwa ofishin ‘yan sanda, ko a bIO, kai har ma kotu na kan je na tashe tsaye sai na tabbatar da wannan lamari ya wuce, kuma a lokacin ma ina karkashin wani, to irin wadannan halaye nawa suka gani suka ce lallai ni ya dace na jagorance su a matsayin shugaba, domin wannan aikin da yakama shugaba ya yi, To wannan zabena da suka yi ya sa aka tabbatar da ni a matsayin manaja.

Harkar jama’a tana da wahala, yau idan mutum ya zo gabanka ya nuna baya sonka, to kama ya yi ka tsaya ka yi tuananin me ya say a nuna maka hakan, idan ka yi nazarinsa daga nan kuma sai ka yi tuananin shin tsakanin kai da shi waye ya fi tunani, to yawanci idan ka zo ka yi min wadannan kamalaman na kan tsaya wan a ga kai din nan waye, to daga nan ne zuciyata za ta gaya min abin da zany i. to akasari na kan tsaya na yi abin da ya dace, a nan ne sai mutane su ce gaskiya na yi aiki da basira, kuma har zuwa yanzu dai muna nan a kai.

Shin wane kalubale ka taba fuskanta a wannan aiki naka?

To kalubalen da na fuskanta gaskiya yana da yawa, kai kanka mai tambyar a shekarar da ta gabata ka zo ka same ni cikin wani yanayi na bacin rai a nan Mararraba, lokacin da aka zo aka rushe garejinmu aka zo aka farfasa min motoci, wadanda suka yi abin abokan aikinmu ne, NURTW ne suka hade da wasu ma’aikata na Hukumar Bunkasa Birane ta Jihar Nasarawa wato ‘Nasarawa State Urban Debelopment Board,’ to wanda aka hada bakin da shi a halin yanzu shi Allah ya yi masa rasuwa, kuma har ya zuwa yanzu ina cikin wannan yanayi sai dai hakuri kawai muke yi, to hakuri ne jigon samun nasarata.

kalubalen da samu a lokacin shi ne, an farfasa mana motoci, kuma a lokacin an sanya dokar takaita zirga-zirga saboda cutar Korona, gashi an rushe mana gareji mun rasa inda za mu tsuguna da inda za mu ajiye motocin gwamnati. To daga karshe sai muka dawo nan ‘Muhammadu International Market,’ suka bamu mafaka kamar yadda ka gani har yanzu. Amma dai har yanzu bamu da wani tabbataccen garejin da za’a ce wannan na gwanmati ne na jihohin Arewa maso Gabas da suke amfani da shi, wanna shi ne kalubalen da muke ciki har yanzu.

Wadanne irin nasarori ka samu da ba za ka iya mantawa da su ba?

Gaskiya a shekarun baya lokacin da muke zaune a wancan garejin bayan an zabe ni a matsayin shugaba na motocin bas na gwamnati, mun samu ci gaba sosai, a lokacin na sa an yi mana kungiya, kuma ni na tashi da wasu mambobinmu zuwa wasu jihohin Arewa kamar Jihohin Gombe, Bauchi, Taraba, Yobe, Maiduguri, da kuma Folato, muka nemi hadin kan su ma’akatan da kuma direbobinmu. A lokacin sun bamu cikakken hadin kai sosai wanda kuma mun tara abubuwa sosai da ba’a taba yi ba.

Ka yi maganar baku wani kebantaccen wuri na gwamnati da zaku ajiye motocinku, wane kira za ka yi ga gwamnatin Jihar Nasarawa?

To ni abin da nake so mai yiwuwa ba shi ne ra’ayin gwamnatin ba, amma da son samu ne, a nemi wurin gwamnati inda motocin gwamnati ke zama, kamar a Adamawa muna da tasha ta NURTW, wacce gwamna ya gina, mu ma muna da namu daban ba’a taba hadawa ko da Union a wani lokaci ba, a Gombe ma haka, Taraba ma haka. To ina rokon gwamnatin Nasarawa ta taimaka idan wannan wurin tasha ce, to a tabbatar da cewa wannan tashar tamu ce wannan ta tsallake, ta kusa da International market, a mallaka mana ita.

To gashi an samu wata kafar yada labarai ta karrama ka, me z aka iya cewa kan hakan?

Wallahi na ji dadi kawarai da gaske, lhamdulillahi na godewa Allah nag ode musu bias tunanin da suka yi, jiya da suka aika min da sakon za su bani lambar yabo na yi ta tunani, sai kawai na ji murna na kwana da murna kuma Allah ya tabbatar yau sun bani, Allah ya saka musu da alheri, Allah ya bar zumunci. Kuma yanzu sun kara min kaimi ne nag ode Allah ya saka da alheri.

Kuma yanzu zan kara hazaka kana bin da na yi a baya, in na taimako ne in sha Allahu zan kara a kai madalla nagode.

Dahiru Abubakar Tula a tsakiya yana karbar lambar yabo, daga damansa Sadau Bala, daga hagunsa, Abubakar Kare, sannan Sulaiman Sango

Exit mobile version