Daga Muh’d Shafi’u Saleh,
A wani shirin bunkasa noma domin samar da abinci, mamba mai wakiltar kananan hukumomin Numan, Demsa da Lamurde a majalisar wakilai ta kasa Kwamoti La’ori, ya bada tallafin kayan aikin gona ga manoma a yankin mazabu 30, da ke kananan hukumomin uku.
Kayayyakin sun hada da buhunan takin zamani, magungunan kashe ciyawa, fanfunan feshin, kyauta da nufin imganta harkokin noma a yankin.
Da yake raba kayan aikin gonar a madadin dan majalisar Mista Pwagwadi Omeno, ya ce kayan yana daga cikin tallafin dan majalisar na tabbatar da ganin harkar noma ya inganta a yankin, domin magance matsalar karancin abinci.
Aikin raba kayan abinci na kwana biyu, ya gudana ne a ofishin dan majalisar na yanki dake garin Numan, wanda ya samu halartan manoma da dama da su ka amfani da shirin a kananan hukumomin uku.
Mista Omeno, ya kuma yiwa manoman alkawarin ci gaba da samun tallafin daga dan majalisar, domin tallafawa mutane da magance talauci da kuma tabbatar da cewa abinci ya samu a yankunan kananan hukumomin da ya ke wakilta.
Da su ke bayyana farin ciki da samun tallafin, manoman su ka ce tallafin ya zo a lokacin da ya dace domin kuwa zai taimaka wajan farfado da harkokin noma da magance matsalar abinci a yankinsu.
Haka kuma Baba Kabin Damara da Pastor James Malik, sun yabawa dan majalisar da cewa “tallafin ya zo a lokacin da ya dace, muna godiya ga Kwamoti La’ori da ya tuna da mu a lokacin da muke da bukata” inji manoman.
Manoman sun kuma yi alkawarin amfani da kayan tallafin yadda ya dace a matsayinsu na magidanta, za su tabbatar tallafin ya amfani iyalansu.