Daga Bello Hamza, Abuja
Shugaban hukumar FRSC na yankin jihar Ogun, Mr Joseph Akinsanya, ya yi alkawarin tabbatar da ganin an samu raguwar hatsurra a kan hanyoyin kasar nan.
Akinsanya ya yi wanan alkawarin ne a tattaunawarsa da manema labarai a garin Ifo ta jihar Ogun ranar Juma’a.
Shi dai Mr Joseph Akinsanya, ya karbi aiki ne daga hannun Mr Joshua Ibitimi wanda aka tura aiki jihar Legas shi kuma ya taso ne daga jihar Imo.
Ya kuma yi alkawarin samar da hadin kai da sauran bangarorin jami’an tsaro don samun wannan nasarar.
“Muna da shirin gudanar da shirin gangamin fadakar da kan al’umma a yankin Ifo don ilimantar da al’umma bukatar amfani da hanyoyimu yadda ya kamata don kaucewa asarar rayuka da dukiyoyin al’umma.
“Za kuma mu tabbatar da ana bin ka’idoji da dokokin hanya a manyan hanyoyinmu,” inji shi.