Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya (NIS) ta sanar da ƙarin kuɗin yin Fasfo, wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga Satumba, 2025.
A wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, ACI AS Akinlabi, ya fitar a ranar Alhamis, an bayyana cewa wannan sabon tsari zai shafi aikace-aikacen da ake yi ne kawai a cikin Nijeriya.
- Nijeriya Za Ta Ɗaukaka Da Fasahar Ƙere-ƙere Da Tattalin Abinci – Tinubu
- Gwamnan Katsina Ya Dawo Gida Domin Ziyara Ga Al’ummar Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Wa Hari A Malumfashi
Sabon tsarin ya ƙayyade kuɗin fasfo na shafuka 32 mai ingancin shekaru biyar a kan N100,000, yayin da na shafuka 64 mai ingancin shekaru goma zai kasance N200,000. Sai dai an bayyana cewa kuɗin da ake biya ga ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje ba su sauya ba, inda ake cajin $150 ga shafuka 32 da $230 ga shafuka 64.
Hukumar ta ce wannan mataki na da nufin kare inganci da sahihancin Fasfon Nijeriya tare da tabbatar da cewa ƴan ƙasa suna ci gaba da samun damar amfani da shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp