Daga Dakta Jamil Zarewa,
Assalamu alaikum, Malam don Allah ina da tambaya ni nurse ce to ina aiki aka kawo min ‘patient with respiratory distress’ na daura shi saman ‘odygen therapy’ sai yake min koken yana jin ciwo, ya rasa inda zai sa kan shi ya ji dadi, sai na kira Likita don ya zo yaji kokensa, na ji bai zo ba, sai na rubuta mashi allurer ‘paracetamol injection’ da ‘diazapem’ don ya samu ya yi bacci, ina ba shi allurar sai yanayinsa ya canza sai ya fara ‘gasping’ bai dade ba ya ya rasu, na san lokacin shi ne ya yi, amma sai ni ke tunanin ko allurer da na ba shi ita ta sa ciwon ya kara rikecewa, sai na yi ‘browsing internet’ sai na ga a she ba’a yi ma mai ‘respiratory distress diazapem.’
Tambaya ta shine zan yi azumin kaffara ne koko tun da ni na yi ne don in taimake shi ban san tana da illa ba? Na gode.
Wa alaikum assalam. Za ki yi kaffarar kisan kuskure saboda a ka’idar likitanci ‘Nurse’ ba sa ba da magani ko Allura sai da iznin likita ko shiryarwarsa, ke kuma kin kuskure kin ba shi maganin da bai kamata ya sha ba kafin likitan ya zo, kamar yadda kika yi bayani, don haka ke ce kika zama sababin mutuwarsa.
Rayukan mutane amana ne, ya wajaba Likitoci su yi taka-tsantsan wajan zama sababin salwantarsu, gushewar dakin Ka’aba ya fi sauki a wajan Allah fiye da kashe Musulmi.
Idan likita ya yi sakaci wajan TIYATA, ko kuma hada magani ko ya kuskure wajan abin da ya kamata, har mara lafiya ya mutu, zai yi kaffara, saboda kisa ne na kuskure, kisan kuskure kuma ana yi masa kaffara kamar yadda Allah ya yi bayani a aya ta (92) a Suratun Nisa’i.
Za ki yi kaffara ta hanyar biyan diyyar rai da kuma Azumin watanni biyu a Jere.
Allah ne mafi sani
Zan Iya Shafa Magani Saboda Gemu Ya Fito Don Tsayar Da Sunnah?
Assalamu Alaikum Allah ya kara wa Dr lafiya, ina da tambaya: Shin ya halatta mutum ya shafa cream domin gemunsa ya fita ya tsayar da SUNNAH?
Wa alaikum Assalam, zai fi kyau ya jira har Allah ya fito masa da shi, saboda amfani da magungunan da suke canza yanayin dan’adam yana biyar da matsaloli a mafi yawan lokuta.
Allah yana iya ba ka ladan wanda ya tsayar da gemu ko da bai fito ba, mutukar niyyarka ingantacciyya ce.
Allah ne mafi sani.
Babana Yana Nuna Mana Bambanci Da ‘Ya’yan Kishiyar Mamanmu, Ina Mafita?
Assalaamu alaikum. Malam Allah ya kara maka imani da fahimta Tambayata itace Mahaifina ne yake nuna banbanci a tsakaninmu sannan yana yawan zagin mahaifiyata musamman in kannena sun yi masa laifi sai ya kama zagin ta sai na nuna masa rashin jindadina da wannan al’amari har ya kai ga mun daga ma juna murya. Karshe sai ya fara yi min Allah ya isa yana tsine mun. Me ya kamata na yi yanzu?
Wa’alaikum salam. Ya wajaba uba ya yi adalci a tsakanin ‘ya’yansa, Annabi (SAW) yana cewa : “Ku ji tsoron Allah ku yi adalci a tsakanin ‘ya’ya yanku” Wannan ya sa lokacin da Sahabi Bashir ya yi wa dansa kyauta, ya nemi Annabi (SAW) ya yi shaida a kan haka, ya tambaye shi : shin duka ‘ya’yanka ka yi musu kyauta? sai ya ce a’a, sai Manzon Allah ya ce : Ba ka so su zama daidai wajan yi maka biyayya? Ba zan yi shaida a kan zalunci ba”. Bukhari da Muslim sun rawaito wadannan riwayoyi.
Yin adalci a tsakanin iyalai yana inganta tarbiyya, yana sanyawa su ji tausayin Uba bayan ya girma, yana kara musu hadin kai da son juna.
Ya wajaba mazaje su sani cewa : zagin matayensu ya saba wa ka’idojin shari’a, kuma hanya ce ta tabarbarewar tarbiyya, domin Yaran za su rabu biyu, wasu suna bayan mahaifinsu, wasu kuma Babarsu za su ga ta yi daidai.
Kai kuma nasihata gare ka ita ce, ya wajaba a tausasa harshe lokacin da za a yi magana da mahaifi saboda Allah ya hana fada wa Uba kalma mara kyau ko yaya take, kamar yadda ya zo a Suratul Isra’i.
Kai ma Uba, ya kamata ka sani ba a son ana yın muguwar addu’a ga iyalai saboda in aka dace da lokacin amsar addu’a za ta zamar masa matsala.
Allah ne mafi sani.
Malam Su Wane Ne Allah Ya Ce A Bai Wa Zakka?
Assalamu Alaikum, Dan Allah ina da tambaya ita zakka akwai wanda Allah ya lissafa a ba, ko ko kai za ka ba wanda ka ga dama? Na gode Malam.
Waalaikumussalam. Akwai su mana, a cikin suratu Attaubah, Allah ya yi umarni a bai wa nau’ukan mutane takwas:
1. Fakirai.
2. Miskinai.
3. Wadanda ake fatan jawo zuciyarsu zuwa Musulunci
4. Bayin da aka dorawa fansa, suke neman yadda za su biya.
5. Wadanda ake bi bashi.
6. Wadanda suke raba Zakka.
7. Dan tafarki Wanda kudinsa suka Kare.
8. Wanda yake aikin daukaka kalmar Àllah.
Allah ne mafi sani.