A tattaunawarsa da wakilinmu, Sabo Ahmad, shugaban kungiyar tsofaffin daliban babbar makarantar gwamnati ta Kafin-Maiyaki na kasa, Honorabul Yahaya Yunusa Daba, ya bayyana kokarin da kungiyar ta su ta yi na samar wa da makarantar ci gaba da hada kan tsofaffin daliban a duk inda suke a kasar nan. Haka kuma shugaban ya bayyana irin kalubalen da suke fuskanta. Sannan kuma ya yi kira ga tsofaffin daliban, da daliban da wadanda ke karatu da kuma malaman makarantar kan kowa ya bayar da gudummowarasa don dorewar ci gaban da aka samu Ya kuma roki gwamnatin jihar Kano kan wata muhimmiyar bukatar makarantar.
Honorabul za mu so ka ba mu tarihin wannan kungiya ta tsofaffin daliban babbar sakandiren gwamnati ta Kafin-Maiyaki.
Mun kafa wannan kungiya ne a shekara ta 1993, da nufin hada kan tsofaffin dalibanmu don taimaka wa makaranta da kawunanmu da malamanmu da kuma daliban da ke karatu a makarantar.
Wane lokaci ne ka zama shugaban wannan kungiya?
Na zama shugaba ne tun lokacin da muka kafa wannan kungiyar. Abin da kuma ya sa na zama shugaba tun a wancan lokacin shi ne, irin gudunmowar da su, tsofaffin daliban suka ga na bayar ta kai-komo da tuntuba, har sai da na tabbatar an samu nasarar kafa ta. Daga nan ne suka yanke shawarar in jagoranci kungiyar.
Lokacin da ka zama shugaba, a wancan lokacin me kungiyar ta fara tunkara?
Abin da muka fara yi shi ne, kokarin tattaro mambobinmu, domin hada kawunanmu, ta hanyar kiran taro na farko, wanda kuma mun samu nasarar halartar mambobinmu daga ko’ina a fadin kasar nan.
Daga wannan fa?
Dagan an sai muka yi kokarin aiwatar da wata daga cikin manufofin kungiyar na taimaka wa makarantar. A nan mun yi nasarar gyara tare da samar da abin zama ga wadansu ajujuwa. Da haka kungiyar ta fara har muka dade har muka ci gaba da jagorancinta. Da yake dan Adam tara yake bai cika goma ba, da yawa daga cikin shugabannin da aka zabe mu tare da su, ba su iya daure wa ba, don ci gaba da tafiyar. Bayan da tafiya ta yi tafiya, sai muka sami rauni a tafiyar, inda kungiyar ta yi dogon suma.
Ya ya aka yi ta farfado, kuma har ta cigaba da wanzuwa a halin yanzu?
Bayan la’akari da wadansu daga cikin tsofaffin daliban irin su, Sabo Ahmad da [an’asabe Abdullahi da [an’lami Usman da Mustafa Ali da Balarabe Abdullahi da Muhammad Adamu da Ahmad Shu’aibu da Umar Yusuf da Abubakar Umar, suka yi na muhimmancin kungiya, sai suka kafa kwamitin farfado da ita. Kuma Alhamdulillahi hakar su ta cim ma ruwa.
Bayan farfado da ita, sai aka bayar da shawarar cewa, ya kamata a yi zabe, kowa ya amince da hakan. Amma aka ce a bari sai a babban taron kungiyar na shekara-shekara, sannan a sanar da dukan mambobi, domin bai wa kowa damar zaba ko a zabe shi.
Lokacin da aka hadu domin gudanar da wannan zabe, sai tsofaffin daliban suka yi ittifakin cewa in ci gaba da shugabancin kungiyar, sai aka zaba min mataimaka,
Daga nan kuma ya wannan sabon zubin ya kasance?
Daga nana ne muka fara kai ziyara gurare daban-daban, don kara kulla zumunci a tsakaninmu, inda muka je Doguwa da Tudun-wada da Bebeji da {iru da Chiromawa da kuma Kura, domin kara farfado da ruhin kungiyar. Sannan duk inda wani abu ya samu wani daga cikin mambobinmu, in na alherine mu je mu taya shi murna, in kuma na bakinciki ne mu je mu kasance tare da shi wajen nuna bakin ciki akan abinda ya faru.
In na fahimce ka, bayaninka na nuna cewa, ruhin kungiyar ya farfado, bayan farfadowarta me kuma kuka fuskanta?
Gaskiyar kasancewar na samu abokan aiki, wadanda suka bayar da lokacinsu da dukiyarsu don ganin mun sami nasara, sai kungiyar ta ci gaba da bunkasa, ta fuskar gudanar da tarurruka da taimaka wa makarantar.
Bayan wannan sabon lalen, wadanne nasarori za ka iya bayyanawa, wadanda kuka samu a wannan kungiya?
Muna cikin shugabancin ne muka yi ta kokarin hada naira da kwabo na ganin cewa, mun rage wadansu matsalolin da suka addabi makarantar, domin ta kai ko’ina yana bukatar gyara a makarantar, wani lokaci in mun zo taron, muka kwatanta yadda makarantar take a baya da wannan lokacin sai mu yi ta kukan zuci, saboda mun tabbatar da cewa, matsalolin sun fi karfin naira da kwabo.
Daga nan sai muka fara tuntubar mambobin da muka san Allah ya hore musu kumbar susa, domin su kawo dauki. Cikin ikon Allah [anlami Usman ya tuntubi Aisaru Harisu, kan cewa ga fa matsalolin da ke gabanmu. Nan take ya ce, a yi kiyasin duk abin da za a kashe a mayar da Block din da ya zauna sabo. Haka aka kawo kiyasi , ya bayar aka yi wannan aiki, sai ya zama wannan Block din ya zama tauraro, a dukkan makarantar, daga nan muka kara jin dadI, domin nasarar kungiyar ta fara bayyana.
Ana cikin haka sai ga wata babbar dama ta samu, na samu nasarar zama dan majalisar dokoki ta jihar Kano, kuma na kasance ina da kyakkyawar dangantaka da gwamna Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso. Saboda haka sai kaya suka tsinke a gindin kaba.
Dagan an sai muka fara shawarar yadda za mu tunkari gwamna da wannan matsala. Alhamdulillahi, mun je mun tattauna da gwamna kuma ya yi alkawarin zai gyara mana makarantar, a lokacin da za fara gyaran ne ma, wata rana kwatsam sai ga shi ya kawo ziyara ba-zata makarantar don ya ga halin da take ciki, ya zo har sau biyu, domin ya kara tabbatar da gyare-gyaren da za a yi.
Daga nan sai ya bayar da umarni a fara wannan aik. An fara gyara azuzuwa, sannan dakunan kwana sannan kuma aka tafi gidan malamai.
Ya ya kake ji a ranka musamman da yake a lokacin mulkinka ne aka samu wannan gagarumar nasara?
Ai ba zan iya kwatanta farin cikin da nake yi ba, duk lokacin da na tuna wannan nasara. Daga cikin abubuwan da muke nema a yi har da katange makarantar musamman saboda dalilan tsaro, amma dai cikin ikon Allah har gwamnatin ta shude, ba a samu damar yi ba. Amma har yanzu ba mu yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da neman a katange mana makarantar a wannan gwamnatin.
Baya ga wannan babbar nasara sai kuma wacce, tunda ka ce nasarorin da yawa.
{warai kuwa , wata nasarar da muka samu , ita ce, ta taron da muke shekara-shekara, mun gayyato tsofaffin malamanmu, irinsu, Malam Ibrahim [anyaro da Malam Abdu Bompai da Malam Adnan Zubairu da Malam Habu Aba Ari da Mista Emanuel Ediga, da Malam Mustafa Bashir da Malam Umar Othofo, wadanda hada fuskokinmu ya dada tuna mana baya. Baya ga wannan mun sami nasarar rubuta wani littafi “How to Locate Me” tare da kaddamar da shi, wanda ya kunshi sunayen tsofaffin dalibanmu guda 200 da adireshinsu da kuma lambobin wayarsu. Samar da littafin ya ba tsofaffin dalibanmu damar samun sassaukar hanyar sada zumunci.
Bugu da kari mun yi bikin cika shekara talatin da kafa makarantar, inda muka gayyato shugaban makarantar na biyu, watau Malam Habu Aba Ari da wadansu tsofaffin malaman makarantar da aka bude ta da su. Mun shirya ziyara tare da kai tallafi ga iyalan marigayi, shugaban makarantar na farko Malam Awwalu Abubakar da ke Zangon-Daura a jihar Katsina.
A kokarin ci gaba da tallafawa makaranta da daliban da ke karatu, Sakataren wannan kungiyar Sabo Ahmad ya bayar da kyautar littafin koyon kwamfyuta guda dari ga makarantar domin amfanin dalibai.
Wane kira kake da shi, ga tsofaffin daliban wannan makaranta?
Kira na garesu shi ne, mu ci gaba da kokarin taimaka wa wannan makaranta wadda ita ce jigon dukkan wani matsayi da za mu samu a rayuwa. Sannan kuma mu taimaka wa junanmu.
Wace shawara kake da ita ga daluban da ke karatu a makarantar a halin yanzu.
Shawara ta garesu ita ce, su dage da karatu yadda za su samu nasarar cin jarabawowinsu. Sannan su kasance masu ladabi da biyayya ga malamansu da sauran daliban da ke gaba da su.
Domin in suka dubi tarihin wannan makaranta ta yi fice wajen samar da dalibai masu kwazo da da’a, wanda hakan ta sa, tsofaffin daliban ke bayar da gagarumar gudunmowa wajen bunkasa kasa da rayuwar al’umma.
Wane kira ka ke da shi ga gwamnati?
Kira na ga gwamnatin jihar Kano shi ne, kan maganar katange wannan makaranta. Gaskiya makarantar na da tsananin bukatar a katangeta, musamman saboda tsaron lafiya da kuma dukiyoyin dalibai da malamai.
Honarabul mun gode.
Ni ma na gode.