Shugaban kasa Muhammadu, Buhari ya ce zai yi amfani da sauran watanni hudun da suka rage masa a matsayin shugaban kasa don jajircewa kafin ya mika mulki.
Ya yi wannan alkawarin ne a ranar Litinin a Damaturu yayin da yake jawabi a fadar Sarkin Damaturu, Hashimi II El-Kanemi.
- Xi Ya Jaddada Muhimmancin Karfafa Cikakkun Managartan Akidun Gudanar Da Jami’iyyar Kwaminis Ta Kasar Sin
- An Tabbatar Da Bacewar Fasinjoji 31 Bayan Kai Hari Kan Jirgin Kasa A Jihar Edo
Da yake tsokaci kan harkae tsaro, Buhari ya bukaci ‘yan Nijeriya da su kara samun yakini duba da yadda jami’an tsaro ke samun nasarar yaki da ta’addanci a Nijeriya.
“A sauran watanni hudu da ya rage min a matsayina na shugaban kasa, zan ci gaba da dagewa kuma ina fatan na yi ritaya cikin kwanciyar hankali,” in ji shi.
Shugaban ya kuma bayyana cewa gwamnati ta dukufa wajen kare hakkin yaran Nijeriya kan samun ilimi musamman wadanda Boko Haram ta raba da gidajensu.
Ya ce, ”Mun sha fama da yawa a kasar nan, amma zan yi kira gare ku da ku dage da kuma tabbatar da cewa ba ku bari wani ya sake wargaza mu ba”.
Ya nuna jin dadinsa da dawowar zaman lafiya a Jihar Yobe da kuma Arewa maso Gabashin Nijeriya.
Ya danganta wannan zaman lafiya da hazakar gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe da takwaransa na Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum.
A cewar Buhari, shugabannin biyu, sun jajirce wajen sake gina makarantu, cibiyoyin lafiya da cibiyoyin da bata-gari suka lalata.
Idan dai za a iya tunawa Buhari a ‘yan kwanakin nan ya yi fatan kammala shugabancin kasar nan domin zai yi nisa da Abuja da kuma sha’anin mulki.
Ya kuma bayyana cewa zai koma jiharsa ta Katsina wadda ke kan iyaka da Jamhuriyar Chadi domin ci gaba da rayuwa.