Daga Ali Bako Kawaji
Da ya ke mu na baya-bayan nan ne, ba mu san yadda a ka gudanar da zabe a Jamhuriya ta farko ba. Sai dai hakan bai hana ni jin labari da kuma karanta tarihin yadda zabukan da aka gudanar a lokacin su ka kasance ba.
Daga 1979 ne aka fara gudanar da zabuka a kan ido na, kuma na fara fahimtar irin gagarimin aiki da nauyin da gwamnati ke dora wa Hukumar Zabe, wato alhakin shirya tsare-tsaren gudanar da zabe domin ginawa ko kafa gwamnatin dimokradiyya.
Tun daga ranar da na fara jefa kuri’a a 1979 zuwa yau, ban taba yin fashin jefa kuri’a a kowane zabe ba. Don haka na san irin Jan aiki da wahalhalun da ke tattare da aikin zabe, wadanda yawanci duk son rai da son kai na ‘yan siyasa ne kan haifar da matsalolin.
Tashin farko ku lura Hukumar Zabe ce ake dora wa alhakin yi wa su kan su jam’iyyu rajista. Sannan kuma za ta gindaya sharuddan da ‘yan takara za su cika da kuma siradin da kowanen su zai tsallaka kafin ya cancanta fitowa takara, kamar yadda dokar kasa ta tanada.
Har ila yau, su kan su masu jefa kuri’a, akwai shirgin nauyin su da dokar kasa ta lafta a kan Hukumar Zabe. Za ta wayar musu da kai dangane da ka’idoji, kuma za ta zaburar da su domin su fito su yanki katin zabe.
Kai, daga ranar da aka ce an kada kararrawar fitowa yakin neman zabe, to daga wannan ranar babu sauran barci a idon Hukumar Zabe, har sai bayan ta kammala dukkan zabukan da ke gaban ta, ta bayar da satifiket ga wadanda su ka yi nasara.
A nan ma barcin ba zai yiwu ba, domin masu korafe-korafe ba za su bar Hukumar ko dan gyangyadawa ta yi ba. Me zai karance, daga nan ne daruruwan masu korafi za su rika garzayawa kotu a sukwane su na kai karar rashin amincewa da ko dai sakamakon zabe, ko kuma su kai karar rashin cancantar dan takarar da ya kayar da su.
Kun san Hausawa sun ce zomo ba ya fushi da makashin sa, sai maratayin sa. Duk wanda zai kai karar dan takara, to sai ya hada da Hukumar Zabe, ita ma ya maka ta kotu.
Don haka ni ban yi mamaki da Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa sau 700 ana kai hukumar zabe kara a cikin wani kankanen lokaci ba.
Domin tabbatar da dorewa dimokradiyya, abu ne mai muhimmanci masu kada kuri’a da kuma musammam su ‘yan siyasa su gamsu da cewa lallai hukumar zabe ita ce ginshiki, tubali, tushe, bangon jingina, sannan kuma ita ce gishirin miyar dimokradiyya. Martabar hukumar zabe ita ce martabar dimokradiyya.
Hukumar zabe gada ce wacce sai shugabanni sun hau ta kan ta sannan za su kai bisa kujerar mulkin jama’a. Haka su ma jama’a, Hukumar Zabe ce jirgin ruwan da ke yi musu fito domin ya kai su a kan tsandaurin zaben wanda duk su ke so ya kafa musu mulkin na dimokradiyya.
Babbar matsalar da Hukumar Zabe ke fara cin karo da ita, shi ne rigingimun ‘yan siyasa a cikin jam’iyya yayin tsayar da dan takara. Irin yadda wasu shugabannin jam’iyya ke tsayar da ‘yan takara a yayin zabukan su na fidda-gwani, kan haifar da rikita-rikitar jamgwangwamar da ko da Hukumar Zabe ta gudanar da zabuka na bai daya, to daga baya sai a ji an kaure da korafe-korafe, har ma an garzaya kotu.
Rikicin baya-bayan nan da ya faru tsakanin Sanata Dino Melaye na jihar Kogi da shi da ‘yan mazabar sa, ba rikici ba ne tsakanin sa da INEC. Hukumar Zabe ba ta da wata matsala da Sanata Dino Melaye. Su ne su ka zabi abin su, kuma a yanzu su ka ce ba su son abin su, ya koma gida. Ashe kenan tunda gadon bayan Hukumar Zabe su ka taka sannan su ka dora Melaye a majalisa, to fa tilas sai sun sake taka gadon bayan hukumar sannan za su iya kakkabo shi ya fado kasa. Bahaushe ya yi gaskiya da ya ce “ta inda aka hau, ta nan a ke sauka.”
Ita da INEC ta na da sharuddan ta na yi wa wakilin al’umma kiranye daga majalisa ko ta tarayya ko ta jiha. Kuma ta na da matakai wadanda sai an bi ta kan shimfidar su sannan za a nemi Hukumar Zabe ta zo ta domin a hau gadon bayan ta a sauko da wakilin da aka kai a majalisa.
Don haka, matsawar al’ummar yankin nan sun cika sharuddan yi wa wakilin su kiranye, to fa babu wani dalili da wani ko wasu siyasa za su rika shigewa gaba a cikin duhu ko a bayyane su na gina ramuka a gaban INEC domin ta fada ta gurje guiwa ko ta yi targade ko kuma ta karye kafafu.
Don me za ka garzaya kotu ka kai karar Hukumar Zabe, don ta aika maka sammacen sanar da kai cewa za ta yi aikin ta a kan ka na yi ma ka kiranye kamar yadda dokar kasa ta umarce ta?
Shin Dino Melaye bai sha bada goyon bayan kafa dokoki a kan wasu ba? Mene ne laifin INEC tunda aikin da aka sa ta za ta yi a kan ka?
Bai kamata duk masu kishin dimokradiyya su rika zuba ido wasu na watsa wa Hukumar Zabe barkono a gaban ido ba. Idan Hukumar Zabe ta makance, to masu jefa kuri’a da shugabanni da ita kanta dimokradiyya din duk makancewa za su yi.
Na yi mamakin yadda har ita kan ta jam’iyyar APC ta maka INEC kara a kotu domin hana yi wa Dino Melaye kiranye.
Alhamdu lillahi ganin yadda Nijeriya ta kara yin dace da ingantacce kuma mutum nagari a shugabancin Hukumar Zaben kasar nan. Farfesa Mahmood Yakubu ya gudanar da zabukan da dama tun farkon zaman sa Shugaban INEC na kasa zuwa yau. Da yawan zabukan kuma sun fi na wadanda ya gada inganci.
Kwarewar sa da kuma sanin muhimmancin dimokradiyya ya kara gina hukumar a kan turbar bin umarni da kuma biyayya ga kotu. Dama haka ake so duk shugaba mai kaifin hangen nesa ya rika tafiyar da hukumar da ya ke shugabanci. Ya cancanci a jinjina masa ganin yadda ya nuna ba wanda ya isa ya zare wa INEC ido ya kawo mata cikas a ayyukan ta.
Irin yadda INEC ta aike wa alkali dalilan rashin dacewar kotu ta hana ko ta haifar da jan-kafa wajen yi wa Dino Melaye kiranye, ya tabbatar da cewa INEC ita ce gimshikin ingantacciyar dimokradiyya a Nijeriya.
Ya zama wajibi mu fito mu ci gaba da nuna kotu da ‘yan siyaya cewa masu shiga hancin INEC fa, za su iya janyo idanun dimokradiyya ya rika zubar da hawaye. Babu wata matsala tsakanin mu da INEC. Matsala na can tsakanin ‘yan siyasa da kuma kotu.
Sai mun tashi tsaye mun fara hana a tadiye Hukumar Zabe sannan za mu san cewa lallai mu na da kishin dimokradiyya. Idan ba haka ba kuwa, nan gaba ba a san iyakar wadanda za su rika garzayawa kotu su na neman alkalai su hana INEC gudanar da aikin ta ba. Musammam kuma aiki wanda a shafi muradin al’ummar da su ka sha wahalar zaben wakilan su ko shugabannin su.
*Kawaji ya rubuto ne daga Karamar Hukumar Bichi, Jihar Kano.