Rundunar Jamhuriyar Musulunci ta Iran (IRGC) ta ce a ranar Lahadi ta kwace wani jirgin karkashin ruwa mara matuki na Amurka a mashigar Hormuz, wadda ke da matuƙar muhimmanci, yayin da Iran ke ci gaba da toshe mashigar sakamakon yakin Gabas ta Tsakiya da ya ɗauki watanni ana gwabzawa.
A cikin wata sanarwa da rundunar sojin ruwa ta IRGC ta fitar, wadda gidan talabijin na ƙasar ya ruwaito, ta ce dakarunta sun yi nasarar ƙwace wani jirgin ruwa mara matuki na ƙarƙashin ruwa (UUV) na sojojin Amurka.
Rundunar ta ce an gudanar da aikin ne ta hanyar haɗa bayanan leƙen asiri da kuma amfani da fasahar zamani, tana zargin cewa jirgin yana gudanar da ayyukan leƙen asiri a mashigar Hormuz.
IRGC ta bayyana jirgin a matsayin Remus 600, wani jirgin ruwa mai cin gashin kansa da ke aiki a ƙarƙashin ruwa, inda ta ce yanzu yana hannun ƙwararrun jami’an rundunar domin tattaro bayanan da ya nannaɗo acikinsa.
A farkon wannan watan, IRGC ta ce ta kuma kwace wani jirgin ruwa na ƙarƙashin ruwa mara matuki na Amurka a mashigar Hormuz, wadda ke da muhimmiyar rawa wajen safarar man fetur da iskar gas kafin fara yakin Gabas ta Tsakiya a ƙarshen watan Fabrairu, lamarin da ya haddasa cikas ga zirga-zirgar jiragen ruwa.
Iran ta ci gaba da toshe mashigar Hormuz tun bayan ɓarkewar rikicin, yayin da Amurka ta ƙaƙaba nata takunkumin hana zirga-zirgar jiragen ruwa a tashoshin jiragen ruwa na Iran.














