Connect with us

LABARAI

ITF Za Ta Horas Da Matasa 13,000 Sana’o’in Dogaro Da Kai

Published

on

Hukumar “Industrial Training Fund (ITF)” ta bayyana cewar, kafin karshen wannan shekarar za ta horas da matasa da mata da mutane masu nakasa fiye da 13,000, sana’o’i daban daban don dogaro da kansu.
Shugaban hukumar Sir Joseph Ari, ya bayyana haka a taron day a gudanar da wasu jami’an hukumar a garin Jos ta jihar Filato a karshen mako, yana mai cewa, shekarar 2018, shekara ce na samun gaggarumin nasara ga hukumar.
Ari ya kuma kara da cewa, za a fara horas da aiyyukan hannun ne a tsakanin watan Yuli dana Agusta yayin da ake saran kammala horaswar a watan Nuwamba na wannan shekarar.
Shugaban hukumar ya jaddada cewa, a halin yanzu gwamnatoci a faxin duniya sun juyar da alkiblarsu na wannan karnin na 21 wajen horas da al’ummar su sana’o’in dogaro da kai don samar da aikin yi da ximbin jama’armu.
Ya ce, cikin tsare tsaren da aka yi sun haxa da “National Industrial Skills Debelopment Programme (NISDP da “Women Skills Empowerment Programme (WOSEP),” da “Skills Training and Empowerment Programme for the Physically Challenged (STEPC)” da kuma “Air Conditioning and Refrigeration and Designing and Garment Making”
Mista Ari ya kuma ce, a dai dai wannan lokacin kuma za a kuma ci gaba da gudanar da horaswa a kan “Post-Harbest Technikues and Product Debelopment” da “Akua-Culture/Fish Farming Manure Production” da “Crop Production/Greenhouse Technology” da kuma “Poultry Farming” an shirya waxannan horaswar ne don kara bunkasa yabanyar da manona ke nomawa ta hanyar horas dasu hanyoyin akin gona na zamani wadda kasashen duniya ta yarda dasu “Galilee International Management Institute (GIMI) model.”
Ya kuma kara da cewa, an bayar da karfi a bangaren aikin gona ne saboda harkar gona ne mafi yawan ‘yan Nijeriya suka raja’a gare shi kuma shi ne matakin da gwamnatintarayya ke son amfani dashi wajen bunkasa tattalin arzikin kasar nan.
Ana saran za a aiwatar da shirin NISDP a dukka jihohin kasar nan har day ankin Abuja, amma saura shirin za a gudanar dasu ne wasu zababbun jihohi na kasar nan.
Ya kuma bukaci gwamnatocin jihohi da sauran masu ruwa da tsaki das u xauki xawainiyar matasa zuwa wajen horaswar musamman ta hanyar samar musus da kuxaxen wata wata da kuma kuxaxen fara sana’ar a lokacinn da aka kammala karbar horan.
Advertisement

labarai