Jama’ar Jihar Kano sun bayyana shirinsu na yin tururuwa domin fita zaben gwamna da na ‘yan majalisar jiha da za yi a ranar Asabar 18 ga watan Maris, 2023.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake rade-radin cewa za a iya samun tashe-tashen hankula a lokacin zaben saboda farin jinin da akalla jam’iyyun siyasa biyu ke da shi na neman kujerar gwamna a jihar.
- Karancin Kudi: Mun Yi Asarar Kwai Na Biliyan 30 -Masu Kiwo
- Rikicin Zabe: Jihohin 7 Da Idanuwa Ke Kansu A Zaben Gwamnoni
Wasu daga cikin wadanda za su kada kuri’a wadanda Wakilinmu ya ji ra’ayoyinsu a ranar Juma’a, suna da ra’ayin cewa ba tare da la’akari da abin da ake fada ba za su fita don yin zabe.
Wakilinmu da ya zagaya birnin Kano domin jin ra’ayoyin mazauna garin, ya kuma ruwaito cewa, akwai kwanciyar hankali yayin da ake gudanar da harkokin kasuwanci na yau da kullum.
Ya kuma ruwaito cewar jami’an tsaro a shirye suke da suke yayin da suke sintiri a fadin jihar.
Wasu da suka zanta da LEADERSHIP amma ba su ambaci sunayensu na ganin cewa takarar gwamna za ta kasance tsakanin ‘yan takarar jam’iyyar APC, Nasir Yusuf Gawuna, da na jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusif.
Malam Tijjanni Abdulrahman, wanda ya zanta da wakilinmu ya ce: “Mun shirya tsaf domin kada kuri’ar ‘yan takarar da muke so, jita-jitar cewa za a yi tashin hankali shi ne a tsoratar da mu daga fitowa amma hakan ba zai hana mu fita ba.”
Mista Chinedu Ogochukwu ya kuma ba da tabbacin cewa shi da iyalansa wadanda suka kai shekarun kada kuri’a za su fito domin kada kuri’a amma za su yi hakan cikin taka-tsan-tsan, ya kara da cewa, “muna jin rade-radin yiwuwar tashin hankali nan da can amma za mu fara duba lamarin tukuna.
Wata mace da ta amince ta yi magana da LEADERSHIP bisa sharadin sakaya sunanta, ta kuma ce za ta fita domin kada kuri’a, amma ba za ta bayyana wanda za ta zaba ba.
Siyasar Kano dai ta dauki zabi, inda manyan jam’iyyun adawa na APC da NNPP ke kokarin kafa gwamnati a jihar.