Jami’ar Jihar Bauchi Ta Samu Cigaba Cikin Kankanen Lokaci – Farfesa Uba

Duk maganar da za a yi kan ci gaban ilmi a Jihar Bauchi sai an tabo jami’ar Jihar Bauchi da ke Gadau, wato Bauchi State Unibersity  wacce ke da wasu tsangayoyi na shari’ah a garin Misau da sashen aikin gona a Jama’are da kuma sashen mulki a Bauchi inda jami’ar ta ke shirin yaye dalibai kashi na uku. A wannan fanni an ci gaba sosai musamman ganin yadda a ke fama da rashin samun guraban karatu a jami’o’in kasar nan, hakika wannan jami’a ta taka muhimmiyar rawa tun daga lokacin da tsohon gwamna Malam Isa Yuguda ya ginata, yayin da kuma gwamna mai ci a Jihar Bauchi Barista Mohammed Abdullahi Abubakar shima ya ci gaba da lura da wannan jami’a yadda ake kara inganta ta. Kusan watanni biyu gwamnan Jihar ta Bauchi ya amince da nada FARFESA AUWALU UBA na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi a matsayin mataimakin shugaban jami’ar, don haka wakilin mu a Bauchi MU’AZU HARDAWA ya tattauna da shi don jin ta bakinsa game da irin ci gaban da ake kara samu a jami’ar inda take yaye dalibai take kuma tura malamai zuwa kasashen waje da cikin kasa don karo ilmi, ga yadda tattaunawar su ta kasance:

Me za ka bayyanawa masu karatu game da yadda wannan aiki da ka fara ke gudana a wannan jami’a?

Alhamdu lillahi. Assalamu alaikum warahamatullah, sunan Frofesa Auwalu Uba, nine sabon shugaban jamiar jihar Bauchi wanda mai girma gwamnan jihar Bauchi Barista Mohammed Abdullahi Abubakar ya nada kimanin watanni biyu da suka gabata kuma na fara wannan aiki saboda dama a baya ina zuwa a matsayin farfesa mai ziyara ina koyarwa a Jami’ar. Duk maganar da za a yi kan ci gaban ilmi a Jihar Bauchi ba zai cika ba sai an yi maganar wannan jami’a wacce babban ci gaba da na taras shi ne yadda dalibai ke neman shiga wannan jami’a saboda yadda ake samun cunkoso a jami’o’in kasar nan. Duk da cewa hukumar JAMB ta rufe sashen rijistar dalibai amma kullum zuwa suke yi don neman shiga wannan jami’a lamarin da ya sa a kullum aiki ke karuwa garemu don kiyaye duk wata ka’ida da ta dace wannan ya bamu babban ci gaba. A baya wasu kwasa kwasai sai ana zaga wurare ana neman malamai da za su temaka, amma yanzu an wayi gari muna da yara masu yawa da suke son shiga wannan jami’a saboda kullum dalibai suna cin jarrabawar sakandare suna neman gurbi. Don haka a kowane lokaci dalibai na neman gurabe a kwasakwasai don yin karatu a wannan jami’a muna  basu gwargwadon yadda doka ta tsara.

 

Duk wata makaranta idan ta fara aiki tana samun kalubale daga hukumomin da ke lura da su wane kalubale ku ke fiskanta?

Sanin kowane akwai hukumar tantance aikin jami’o’i ta kasa wato Unibersity Commission su ke da hakkin duba yadda jami’a ke gudanar da aikinta da irin kayan aikin ko wurin aiki da ta ke da su da kuma irin daliban da ta ke dauka da ka’idar bin daukar dalibai da kuma yanayin malaman da ake da su da kwas da ake da su da yadda ake gudanar da karatun da irin takardun da malami ko dalibi ke da su wanda sun dace da dokokin hukumar ko akwai gyara. Daga nan kuma bayan shekara biyu sai su dawo don sake duba yadda komai ke gudana domin tantance kwasa-kwasan da yi musu rijista da sauran abubuwan da suka dace da dokoki don samun ingancin takardu da ingancin karatu tun daga farko har karshe sai kun yi rubutu wannan hukuma ta zo ta duba duk irin kayan aiki  da kuke da su da gine gine da sauran wuraren da suka zama na da muhimmanci kafin a amince da karatun da ku ke yi, har da malamai da dalibai da takardun da kowa ya mallaka da abubuwa da dama duk ya na cikin ka’idar da dole jami’a ta cika kafin a amince da ita ko a amince da karatun da ta ke yi a duniya baki daya.

A farko an amince da kwasa-kwasai da dama wasu kuma an musu amincewar wucin gadi wasu kuma sun iso lokacin da za a sake duba kaidojin da suke tafiya a kai. An bude wannan jami’a 2012, amma zuwa wannan lokaci ta na tafiya daidai kamar ta shekara 30 da fara aiki aiki saboda yadda gwamanti ke bayar da muhimmanci tare da samar da kudi da duk wani abu da a ke bukata don ci gaban wannan jami’a da cika ka’idojin hukumar lura da jami’a da sauran hukumomi.

 

Me yasa ku ke mai da hankali wajen gina filayen wasa da ofisoshi alhali dalibai basu da wurin kwana a wadace don inganta tarbiyyarsu?

Bukatun suna da yawa kuma zai yi wahala a dauki abubuwa duka lokaci guda don haka mu ke bin gine ginen jami’ar a hankali saboda bama son yin dibar gonar rani daga karshe aikin ya dagule mana. Don haka muke yin gine gine da suka fi muhimmanci kamar ofisoshi da azuzuwa da filin wasanni da dakunan bincike, kamar yadda doka ta tanada wanda suka fi muhimmanci su muke fara yi mataki mataki. Yanzu haka akwai filin wasan da muke ginawa wanda idan muka kammala shi zai kasance kowane irin wasa na kasa ko duniya za a iya yi a ciki. Kuma gidan kwanan dalibai shima muna yi amma kasancewar daliban da yawa dole mun nemi ‘yan kwangila sun kama wani gefe mun basu fili da ka’idojin irin kudin da za su kashe da kuma ginin da za su yi da yawan shekarun da za su yi suna bayar da hayar wurin kwanan ga dalibai kafin daga bisani idan sun fitar da kudin su da suka kashe sun ci riba sai su mayar da ginin wa hukumar makaranta wannan shima tsari ne da makaranta za ta amfana mutane za su amfana.

Saboda a kullum muna mayar da hankali wajen bayar da tarbiyya wacce ta dace ga daliban mu ta yadda duk inda suka je idan an gan su za a san suna da da’a suna kuma nuna misalai masu kyau da za a yi koyi da su. Don haka muke ba mutane hakuri domin muna bin tafiyar a hankali ta yadda kowa zai amfana ba tare da samun matsala ko ci baya ba. Kuma duk wanda ya ga sassan wannan jami’a da ke nan Gadau da wanda ke Misau wato tsangayar shari’a da ta cikin garin Bauchi inda ake da tsangayar mulki da sauran kwasa kwasai da tsangayar aikin gona da ke Jama’are dole a fahimci cewa Jihar Bauchi ta ci gaba sosai a wannan fanni na bunkasa ilmi.

Kuma duk inda ka tsayar da dalibin mu bama haufi zai iya kare takardar da muka bashi saboda ingancin abin da muka koya masa. Kuma kafa wannan makaranta babban alheri ne a Jihar Bauchi saboda irin ci gaban da aka samu a fannin dalibata da malanta da samar da ayyukan yi. Saboda a halin yanzu muna da malamai masu yawa da ke karatu a kasashen ketare wasu na karatu a cikin kasa don samo duk wata takarda da a ke bukata, don aikin su ya inganta. Muna da masu manyan digirori na dokta da masu kananan digirori a kowane fanni da a halin yanzu ba sai mun rika bin jami’o’i mu na nemo aron malamai ba saboda mai girma gwamna ya na bayar da kudi don yin duk abin da ya dace don kare wannan jami’a da martabarta ta yadda za ta goga da duk wata jami’a da ke kasar nan ko a duniya. Kuma takardun da muke bayarwa kowa ya san suna da inganci daliban mu za su iya kare duk wata takarda da muka basu.

Don haka muke neman mutane su kara hakuri tare da yi mana addu’ah don ganin wannan jami’a ta kai duk wani matsayi da ba a zato wajen ci gaba a duniya kuma nan ba da jimawa ba muna fatar fara yin duk wani irin karatu da ake da bukatar sa idan mun samu kai wag a wannan mataki saboda muna bin lamurra ne a sannu yadda za a samu nasara cikin lokacin da aka ba mu don wannan aiki da muke ganin da yardar Allah ana gamsuwa da yadda muke tafiyar da ayyukan mu da fata Allah ya wuce mana gaba.

Exit mobile version