Gwamnatin kasar Jamus ta bayyana aniyarta ta karfafa dangantakar tattalin arzki da gwamati da kuma al’ummar Jihar Inugu, musamman a bangaren harkar gona, lantarki kasuwanci da zuba jari.
Ta kuma ce, ta zabi Jihar Inugu ne a matsayin wurare uku da za ta mayar da hankalin ta don zuba jari da gudanar da harkokin kasuwanci a yankin kudancin kasar nan saboda yaddd ta lura da harkokin kasuwanci da zuba jari ke tafiya a karkashin gwamnan jihar Dakta Peter Mbah.
- Kudaden ‘Yan Majalisa: Wa Za A Gaskata Tsakanin Hukumar Albashi Da Kawu Sumaila?
- Jihohi Sun Kashe Naira Biliyan 139.92 Wajen Biyan Bashin Kasashen Ketare A Wata 6
Jakadan kasar Jamus a Nijeriya, Weert Börner, ya bayyana haka yayin da ya jagoranci tawagar ‘yan kasuwa da kwararrun kasar a ziyarar da suka kai wa Gwamna Peter Mbah a garin Inugu.
Börner ya kuma ce, ziyarar ta kasance ci gaba ne daga tattaunawar da bangarorin suka yi a garin Legas a shekarar 2023, inda aka nemi a kara samar da hadin gwiwa domin bunkasa zumuncin da ke tsakanin bangarorin biyu.
“Na yi murnar kasancewa a Inugu domin zurfafa tattaunawarmu, na yi murnar kasacewar cikin tawagar mu a kwai wakilin cibiyar masa’anantun mu (DHK Deutsche Handels Kompetenz), da manyan kamfanoni da suka dade suna harkokin ci gaba a Nijeriya, kamar GIZ da Siemens Energy.
“Mun samu labarai daga kafafen sadarwa na Nijeriya wadanda ke nuna cewa, Jihar Inugu ta samar da yanayi mai inganci na zuba jari ga ‘yan kasuwan ciki da kasashen waje.
“Gwamnatin Jamus ta yanke shawarar mayar da hankali ga wasu jihohi na musamman a fadin Nijeriya, jihohin sun kuma hada da Ogun, Abia, da Jihar Inugu, a kan haka muka zo nan yau domin tabbatar da wannan shawarar,” in ji Jakadan.
A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Inugu, Peter Mbah ya mika godiyarsa ga tawagar kasa Jamus a kan yadda suka zabi jihar sa don gudanar da wannan harkokin bunkasa kasa. Ya yi alkawarin bayar da dukkan goyon baya da suka kamata don samun nasarar da ake bukata, ya kuma ce, dukkan bangarorin za su amfana da huldar da za su a tsakanin su a harkar gona, wutar lantar, kasuwanci wanda hakan zai taimaka wajen samar wa da matasan jihar ayyukan yi.