Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello, yace, gwamnatin Jihar ta bayar da hutun kwana daya na yau Litinin 21 ga Agusta, don yin addu’o’i da murnar dawowar shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari gida, bayan shafe kwana 103 yana jinya a birnin Landan.
A cikin sanarwar da Babban mai taimakawa gwamnan jihar Kogi kan kafofin yada labarai Kingsley Fanwo ya fitar yace, an ayyana ranar litinin a matsayin ranar hutu saboda murnar dawowar shugaban kasar.
Gwamna Yahaya, ya bukaci ‘yan jihar da suyi amfani da ranar don yi wa Shugaban Kasar addu’a na samun nasarar ayyukan alkhairi da ya yi wa ‘yan kasar alkawari, kuma ya godewa ‘yan jihar yayin tarbar shugaba Buhari da suka yi Abuja.