Umar A Hunkuyi" />

Jihar Neja ta Samar da Miliyan 260 Don Karfafa Matasa

Gwamna Abubakar Bello na Jihar Neja ya ce, akwai shirin da gwamnatinsa key i na samar da gudummara naira milyan 260 domin karfafan matasa a cikin Jihar.

Wata sanarwa da Sakatariyar yada labarai na Gwamnan, Mary Berje, ta fitar a ranar Asabar, a Minna, tana cewa, Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da kungiyoyin mata da matasa a filin saukan Jiragen sama na Minna, jim kadan da dawowarsa daga Legas.

Bello ya umurci Sakataren gwamnatin Jihar, Alhaji Ahmed Matane, da kuma shugaban ma’aikatansa, Malam Ibrahim Balarabe, da su tsara dubarun da za a yi wajen samar da kudaden.

Ya ce, basukan da za a bayar wadanda bas u da ruwa a kansu, zai taimaka wa gwamnatin Jihar ne ta fuskacin samawa dimbin matasan Jihar ayyukan yi.

Gwamnan ya kuma bayar da tabbacin cewa gwamnatin na shi za ta ci gaba da samar da dukkanin abin da zai bunkasa Jihar.

Ya ce, ziyarar da ya kai a birnin na Legas ya je ne domin nemo masu zuba jari daga sassan Duniya da su zo su zuba jarukansu a cikin Jihar musamman a sashen noma.

Daga nan Gwamnan yay i kira ga matasan da su guji ayyukan bangar siyasa da ta’addanci gami da sauran ayyukan laifi.

Ya umurce su da su kama sana’o’in da za su amfani rayuwarsu su kuma kawo ma Jihar ci gaba da bunkasa.

Ya bayyana aniyar gwamnatinsa na samar da yanayin da ya dace domin karfafan matasan da sauran al’umman Jihar.

Exit mobile version