Rundunar Sojin Sama ta Operation Hadarin Daji ta kashe ‘yan ta’adda 42 a kusa da kauyukan Zakka da Umadan a karamar hukumar Safana ta Jihar Katsina.
A cewar majiyar sojin, wani jirgin saman yakin Nijeriya a yayin da ya ke shawagi a sama, ya samu bayanan sirrin ganin ‘yan ta’adda a tsakanin kauyukan Zakka da Umadan.
- Harin Kuje: Buhari Ya Nuna Rashin Jin Dadinsa Kan Tsaron Kasar Nan
- Da Dumi-Dumi: Mune Muka Kai Hari Gidan Yarin Kuje – ISWAP
Wannan dai na zuwa ne a yayin da ‘yan ta’addan suka kai hari ofishin ‘yan sanda da ke kauyen Zakka a baya-bayan da ke Dutsenma tare da harbe wani jami’in ‘yan sanda har lahira.
A ranar Talata ne ‘yan ta’addan suka kai hari kan ayarin motocin shugaban kasa a jihar.
Wani babban jami’in rundunar sojin sama, ya ce an gano ‘yan ta’adda a wani kauye mai tazarar kilomita 7.1 daga yammacin garin Safana da kuma yammacin kauyen Yartuda.
Ya kara da cewa an kuma ga wasu mutanen garin na guduwa daga kauyen saboda ‘yan ta’addan sun yi awon gaba da wasu daga cikin mutanen garin.
“An yi sa’a, kamar yadda aka yi tsammani, daga baya an ga wadanda aka yi garkuwa da su suna tserewa bayan nasarar da jirgin NAF ya samu na kashe maharan.
“Abin da ya biyo bayan harin ta sama shi ne an ga wasu daga cikin mutanen kauyen da suka watse a lokacin da ‘yan ta’addan suka fara mamaye kauyen suna dawowa.
“Mutanen kauyen sun kuma tabbatar da cewa an kawar da ‘yan ta’adda sama da 24 a hare-hare da aka kai ta sama,” in ji majiyar.
“Saboda haka, an aike da wani jirgin yakin zuwa yankin gaba daya, inda ya ci gaba da shawagi a yankin har zuwa safiyar ranar 6 ga Yuli, 2022.
“Bayan ganin yadda ‘yan ta’adda kusan 18 suka taru a wurin, jirgin ya kai hari. An yi nasarar kashe da dama daga cikinsu.
“Sakamakon da aka samu ya nuna cewa harin ya yi daidai kuma an yi nasara.
“Har yanzu ana ci gaba da kokarin gano tare da lalata sauran maboyar ‘yan ta’addan da ke cikin Katsina da kuma Arewa maso Yamma baki daya,” in ji shi.