Kananan Hukumomi Na Da Rawar Takawa A Cigaban Kasa – Hon Abdul’Aziz

Hon Abddul’Aziz Ahmad Nahuce, shi ne Shugaban Karamar Hukumar Bungudu a jihar Zamfara, a tattaunawarsa da wakilimu Husaini Baba, ya bayyana irin cigaban da ya samu da kuma kudirinsa na ganin ta zamo zakaran gwajin dafi a fadin Kananan hukumomin da ke cikin jihar. Ga yadda ta kasance.

Hon zamuso ka bayyana wa masu karatu kanka da kan ka?

Da farko ina godiya ga Allah ta’ala da ya ba ku ikon kawo mani ziyara don tattaunawa da ni a cikin wannan jarida, wadda zakarar gwajin dafi, kuma ta shiga tsarar sauran jaridu mai fita a kowace rana LEADERSHIP A Yau. Babban fatanmu shi ne ta dore ta yiwa na turanci zara.

A takaice Suna na Abdul’aziz Ahmad Nahuce, zababben Shugaban Karamar Hukumar Bungudu. Kafin in zamo kan wannan kujera ta Shugabancin Karamar Hukuma, na na yi dan majalisar jihar na tsawon shekaru takwas, zango biyu ke nan, kuma na zamo mai bawa gwamna Sharawa, yanzu kuma ga shi Allah ya bani Shugabancin Karamar Hukumata, ina godiya da irin wannan baiwa da Allah ya yi mani.

 

Tun zamanka shugaban Karamar hukumar Bungudu wane aikin ne wanda ya tsaya maka a rai kuma ka kammala shi?

Ayyukan da su ka tsaya mani a rai suna da dama gaske, amma babban aikin da na fara da shi kuma cikin ikon Allah na kammala shi ne matsugunin ita kanta karamar hukumar. Idan karamar hukuma ba ta da matsugunni ingantace babu yadda ma’aikaci zai ji dadin aikinsa, don haka sai na tabbatar na inganta ginin karamar hukumar don samun muhallin da ma’aikata za su zauna cikin dadin rai domin gudanar da ayyukansu. Kuma ba abun alfahari ba, yadda muka maida karamar hukumar nan ko daga ina ma’aikaci ya zo ba zai burin a dauke shi da ga cikinta ba, musamman yadda ta zamo tsara da ga cikin Kananan hukumon kasar nan. Ina alfahari akan haka.

 

Kafin mu zo ayyukan da Majalisarka ta gudanar, shin ko a kwai wasu ayyukan hadaka da kuka yi da gwamnatin jiha?

Lallai kam akwai ayyukan hanyoyi na tituna tsakanin mu da Gwamnatini jiha karkashin jagorancin gwamna Abdul’aziz Yari Abubakar. Mun gudanar da tituna kilomita 26 a cikin Karamar hukumar Bungudu, wanda ya hada da cikin hedikwatar Karamar hukumar da Kwatarkwashi; a cikin wadannan masarautu babu inda za ka taka kasa, duk kwalta ce kuma mai inganci. Kuma yanzu haka ana yin hanyar Nahuce wadda za ta hade da wasu da ga cikin garuruwan Karamar hukumar Kauran Namoda, kuma samar da wadannan hanyoyi arzikin karamar hukumar ya habaka, kasuwanci ya cigaba. Karamar hukuma da jiha na samun karuwar kudin shiga, don idan da hanya ‘yan kasuwa ba sa zulumin shigo ko’ina don gudanar da kasuwancin su. Kuma a cikin ayyukan hadaka da mu ke yi da gwamnatin Jiha akwai samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana. Karamar hukuma da jiha muna iya kokarinmu na ganin wuraren da ba su da wutar lantarki sun same ta don, haka na ke kira ga wadanda ba a kai masu ba da su kara hakuri da ‘yan kudadan da mu ke samu ne mu ke tsakura wajen gudanar da ayyukan.

 

A sashe lafiya wace rawa majalisarka ta taka wa al’ummar Karamar Hukumar Bungudu?

A yanzu haka kun shigo a sa’a don kun iske muna cikin aikin allarar rigakafin yara ‘yan wata tara zuwa sheka biyar. Wannan allura rigakafin kyanda da na shan’ina ko na kwangwalo kamar yadda jama’a ke cewa, ana kaddamar da ita a matakin jiha baki daya, wanda mai girma mataimakin gwamna Malam Ibrahim Wakala da shugabannin sashen lafiya suka jagoranci kaddamar da ita a fadar Mai Martaba Sarkin Filanin Bungudu, Alhaji Hassan Atto. Fatanmu shi ne duk wanda ke da yara daga wata tara zuwa shekara biyar an yi masa wannan allurar rigakafin kyanda. Kuma wannan aikin allurar ba irin na cutar shan-inna bane, wanda ake bi gida-gida. Wannan wurare ake ware wa wanda akalla sun kai 78, kuma cikin yardar Allah an yi wannan aiki kuma an samu nasara, yaran da muke hasashen za su iya kamuwa da cutar duk anyi masu allurer rigakafi. Yanzu haka wannan majalisar tamu a kwanan baya da aka samu annobar sankarau, tun kafin gwamnatin jiha ta kawo mana dauki, mun yi iyaka kokarinmu na dakile ta, ta yadda bata yadu a cikin karamar hukumar ba.

Kuma batun asibitocinmu da dakunan shan magani, karamar hukuma na iyaka kokarinta na ganin ta samar da kwararrun ma’aikatan lafiya da kuma kayan aiki don saukaka wa marasa lafiya. Kuma yanzu haka muna da shiri na musamman don bunkasa harkar lafiya a cikin karamar hukumar.

 

Wane kokari majalisar ka take yi na ganin ta magance bangar siyasa da zaman kashe wando?

To su matasa muna karfafa masu gwiwa kan su koma makaranta, wadanda su ke da karatun kuma muna kokarin samar masu aikin yi. musamman ma na tsaro, kamar aikin Soja, Dan Sanda da sauran makamantan su. Masu sha’awar karatu kuma muna biya masu kudin makaranta gwargwadon abunda muke iya basu, don ba ka cusa wa matashi abunda bai ta shi yi ba, sai ka bashi shawara da karfafa shi a kan karatu; shi mutum shi ke da iko akansa wajen zabar karatu, don baka tursasa masa ka ce lallai ga abinda zai yi. haka ma sana’a, ita ma ba ka tilastawa matasa yin ta, kuma duk matashin da ya zo mu taimaka masa wajan harka sana’a muna iyaka kokarinmu.

 

Ya batun mata, wane alfanu suka samu zuwanka wannan Karamar hukumar?

Yanzu haka mun shirya kungiyoyi don tallafawa mata a karkashin hukumar (CSDP). Na sa an yi masu rijista kowace kungiya domin taimaka masu, kuma wannnan shirin nan bada jimawa ba zai fara da yardar Allah. Taimako mata tamkar taimakon al’uma ne, don za su taimakwa mazajan su da ‘ya’yansu.

 

Wane kokari majalisar ka ke yi don inganta Masarautu da gyaransu?

Masarauta ita ce cibiyar al’umma gwamnati ke amfani da ita wajen isar sako. Dole ne a janyo masarautu kusa da gwamnati. Tuni gwamnatin Jiha ta dauki nauyin gyara masarautar Bungudu, shi ya sa mu kuma muka mayar da hankali wajen gyaran Kwatarkwashi, domin ita ce idanun wannan yankin wanda al’umma ke alfahari da ita.

 

A karshe mene ne kiranka ga al’ummar karamar hukumar Bangudu?

Kirana ga al’umma shi ne su kara bawa gwamnatin jiha goyan baya don aikin da mai girma gwamna ya yi a karamar hukumar Bungudu ko dan haifafan Bungudu abunda zai iya yi ke nan. Ya gyara hanyoyi da makarantu, yanzu haka ana iya maida su jami’a, don wasu jami’oin ba su kai makarantummu ba. Babu abunda za mu cewa gwamna sai godiya, don bai manta da mu ba. Ina kira ga al’umma da su cigaba da bawa gwamnatin hadin kai da yi mata addu’a don samun dawamamen zaman lafiya da karuwar arziki a karamar hukumar mu da Jiha da kasa baki daya.

 

Exit mobile version