Rabiu Ali Indabawa" />

Karancin Lantarki Ya Sa Nijeriya Na Asarar Tiriliyan N10 Duk Shekara, Cewar Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa, sakamakon rashin isasshen wutar lantarki ya sa Nijeriya na asarar hudade masu yawa ta bangaren tattalin arziki, wanda ya kai na naira tiriliyan 10 a duk shekara. A cikin sabon rahoton bankin Duniya, ya bayyana cewa, kasuwancin hadaka da aka yi a tsakanin gwamnati da ‘yan kasuwa a bangaren wutar lantarki wanda aka gudanar tun a shekarar 2013, bai harfar wa kasar da mai ido ba a bangaren wutar lantarki. Bankin Duniyan ya kara da cewa, har yanzu fannin wutar lantarki na fama da matsaloli masu yawa. Ya ce, sakamakon matsalolin da ake samu a fannin ya sa masu ruwa da tsaki sun rasa tsammanin da suke so su cimma a wannan bangare.

Rahoton ya ruwaito cewa, wannan dalilin ne ya sa babu aminci a tsakanin ainihin masu ruwa da tsaki da kuma mutane wajen inganta wutar lantarki. Ya ce, ana bukatar bin wasu hanyoyin wajen magance matsalolin da ke tattari da fannin, dole ne gwamnatin tarayya ta kashe makudan kudade domin tabbatar da an farfado da fannin wutar lantarki tare da gudanar da tsare-tsaren da ya kamata wanda zai sa a sami wutar lantarki mai daurewa a cikin kasar da dai sauran su. Bankin Duniya ya bayyana fannin wutar lantarki musammam ma masu rarraba wutar lantarki a matsayin wadanda suke tafka babban asara.
Ya ce, “fannin wutar lantarki zai iya farfado wa gwamnatin tarayyar Nijeriya tattalin arzikinta wanda ya durkushe sakamakon barkewar cutar Korona.
“Fannin yana bukatar gudanar da wasu kokari wajen tabbatar da kyakkyawan tsari wanda zai samar da damar rarraba wutar lantarki tare da biyan kudade da kuma ci gaba da kulawa da samar da ishasshen wutar lantarki a cikin kasar.”
Rahoton ya ci gaba da bayyana cewa, idan aka yi kokarin gyara fannin zai samar wa gwamnatin kudaden shiga da bunkasa tattalin arziki da kuma inganta raruwar talakawa tare da fitar da su daga kangin duhun da suke ciki na karancin wutar lantarki. Ya ce, idan aka samu nasarar inganta fannin wutar lantarki, zai kasance tsakinya na bunkasa tattalin arziki, musammam ma a bangaren fannonin tattalin arziki wadanda suke ba daga man fetur ba kamar irin su masana’antu da kuma ayyuka.
“Sakamakon karancin wutar lantarki, Nijeriya tana tafka asarar naira tiriliyan 10 a duk shekara daga bangaren wutar lantarki ko kashi biyu cikin kudaden shiga,” in ji bankin Duniya.
A cewar rahoton, Nijeriya ce ta 131 a cikin kasashe masu gudanar da kasuwanci a Duniya a shekarar 2020, wannan ya safu ne sakamakon matsalolin wutar lantarki a Nijeriya. Ya ce, sakamakon rashin wutar lantarki, Nijeriya ce ta 171 a cikin kasashe 190 wadanda suka ci gaba a Duniya, sannan ita ce ta 33 a cikin 46 na kasashen Afirka da ke bangaran Sahara.
Bankin ya ce, “ishasshen wutar lantarki yana da mahimmanci wajen rage talauci. Kashi 47 na ‘yan Nijeriya ba sa samun wutar lantarki, Nijeriya ita ce tafi tafka asara a yankin Afirka, sannan ita ce ta biyu a Duniya bayan kasar Indiya.
“kasa da kashi 40 ba su da damar samun wutar lantarki a cikin kashi 31 na mutanen da ke cikin kasar. A duk shekara ana amfani da wutar lantarki wanda ya kai na 147 kwh, wanda ya yi karanci sosai idan aka kwatanta mutanen da suke amfani da wutar lantarki a kasar.”
Ya bayyana cewa, gidajen da ke samun wutar lantarki suna fuskantar lalacewar kayayyakin wuta a duk kullum ko kuma a wasu lokutan wutar ta dunga kawowa tana daukewa. A cewar rahoton, kashi 40 ke iya amfani da janareta da kuma sauran abubuwan da ke samar da wutar lantarki kamar irin su na’urar wutar lantarki mai amfani da hasken rana da batura, domin su sami hasken wutar lantarki a cikin gidajensu.

Exit mobile version