ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kasar Sin Na Aiwatar Da Manufofin Diflomasiyyarta Don Biyan Bukatun Al’umma

by CMG Hausa
4 years ago
Kasar sin

Kwanan baya wato ranar 8 ga watan Janairun shekarar da muke ciki, aka soma aiki da wasu jerin matakai na zirga-zirgar mutanen gida da na waje a kasar Sin, al’amarin da ya jawo hankalin kasa da kasa sosai, inda a cewar kafafen yada labarai, sabon kokari ne da kasar Sin ta yi domin tabbatar da cewa, an aiwatar da manufofin diflomasiyyar kasar daidai domin biyan bukatun al’umma.

A bara wato shekara ta 2022, annobar COVID-19 ta ci gaba da yaduwa a duk fadin duniya, kana, duniya ta kara fuskantar sauye-sauye masu sarkakiya. Duk da haka, kasar Sin ta ci gaba da aiwatar da manufofin diflomsiyyarta domin tabbatar da muradun jama’ar kasar.

  • Hukumomin Cinikayyar Zimbabwe Za Su Shirya Taron Tattauna Bunkasa Huldar Kasuwanci Da Kasar Sin

A farkon shekara ta 2022, rikicin kasar Ukraine ya barke, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci a tabbatar da tsaron kowane dan kasar dake waje. A ranar 28 ga watan Fabrairun bara, ma’aikatar harkokin wajen Sin ta fara aikin janye ‘yan kasar daga Ukraine. Kuma sakamakon kokarin da aka yi, ‘yan kasar Sin sama da 5200 sun janye jikinsu daga Ukraine zuwa kasashe makwabtanta.

ADVERTISEMENT

A bara kuma, kasar Sin ta yi nasarar shawo kan wasu al’amuran duniya na ba-zata, da yin gargadi cikin lokaci, da gudanar da ayyukan kwashe ‘yan kasar daga yankuna masu hadarin gaske, da kuma kokarin kubutar da mutanen kasar da aka sace.

A dayan bangaren kuma, domin shawo kan yaduwar annobar COVID-19, gwamnatin kasar Sin ta yiwa jama’ar ta sama da miliyan 4.6 dake kasashe 180 alluran riga-kafin cutar, tare kuma da taimakawa ‘yan kasar dake fama da matsaloli dawowa gida. (Murtala Zhang)

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Kasar sin
CMG Hausa
+ postsBio
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugabannin Kasashen Duniya Sun Yi Wa Sin Fatan Alheri A Sabuwar Shekara
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    San Francisco sabon mafarin hadin gwiwar Sin da Amurka ne
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Xi Ya Halarci Kwaya-Kwaryan Taron Shugabannin Mambobin APEC
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Jagororin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Next Post
Yanzu-yanzu: PDP Ta Bukaci Gaggauta Cafke Tinubu Kan Zargin Safarar Miyagun Kwayoyi

Yanzu-yanzu: PDP Ta Bukaci Gaggauta Cafke Tinubu Kan Zargin Safarar Miyagun Kwayoyi

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.