Shugaban ‘yan Nijeriya mazauna yankin Arewa maso yamma na Afirka ta Kudu Mista Chicaodili Nwanedone, ya bayyana cewa, ‘yan Nijeriya masu harkokin kasuwanci a kasar Africa ta kudu na matukar samun ci gaba a harkokinsu na kasuwanci. Shugaban ya yi wannan bayani a zantawarsa da manema labarai a garin Rustenburg, da ke kasar Afirka ta kudu. Ya kuma kara da cewa, ‘yan Nijeriya da dama na gudanar da harkokin karatu a jami’o’i, wasu kuma na aiki a asibitocin yankin.
Nwanedone ya ci gaba da cewa, ‘yan Nijeria sun mallaki kamfanoni fiye da 30 da ke gudanar da hadahadar sayar da motoci da sayar da abinci da gyaran motoci da yin kujeru da sauransu, hakan kuma yana taimaka wa na samar da ayyukan yi ga matasan kasarnan da ke hijira zuwa Afirka ta Kudu dama ‘yan kasar.
Daga nan sai ya kara da cewa, kungiyarsu na taimaka wa ‘yan Nijeriya da shawarwarin irin harkokin da suka dace su yi a kasar, da kuma yadda za su kauce wa fada rikici da mahukuntar kasar.
A karshe, ya shawarci ‘yan Nijeria masu niyyar shiga kasar Afrika ta Kudu da su tabbatar suna da cikakkiyar takardar izini da sana’ar yi, “yin haka zai taimaka wajen kare musu mutunci da tsangwama daga hukumonin kasar” in ji shi. Ya kuma mika godiyarsa ga hukumomin kasar game da hadin kan da suke samu yayin gudanar da harkokinsu.