Bilkisu Yusuf Ali" />

Khadija Bint Usmanu Danfodiyo: Gwarzuwarmu Ta Mako

Dakin Salamawa, inda zuri'ar Khadija su ke a Hubbaren Shehu Danfodiyo.

Khadija ita ce babbar Diyar mujaddadi Shehu Usmanu Danfodiyo, mahaifiyarta kuma ita ce babbar malamar nan kuma sufiya A’ishatu GabDo(Iya-Garka).An haifi Khadija wajen shekarar 1782.

Kafin a aurar da Khadija, mahaifinta Shehu Usmanu da wasu matansa iyayenta su ne suka karantar da ita ilimin Alkur’ani da wasu fannonin ilimin Addinin Musulunci.Khadija ta auri Malam Mustapha Attorodi, wanda ake takaita sunansa da Tafa, wanda asalinsa shi ma daga Musa Jakollo ne, don haka kakanninsu Daya da Shehu Usmanu Danfodiyo.

Malam Mustapha Attorodi yana Daya daga cikin shahararun mutane waDanda suka taimaka wa Shehu Usmanu Danfodiyo ta hanyar karantarwa da rubuce-rubuce. Malam Musdafa Attorodi Dalibin malam AbdullahiDanfodiyo ne, masani a kan fannonin ilimi daban-daban har da ilimin kimiyya, ya yi fice kwarai har ya zama shi ne tabbataccen wanda zai gadi malam Abdullahi ga ilimi.Malam Abdullahi ya amince da ra’ayinsa a kan matsaloli kusan Dari, a lokacin da suke gyaran Diya’u Ta’awili.

Baya ga zaman sa babban malami, Malam Musdafa Attorodi ya kuma zama magatakardan Shehu Danfodiyo.A lokacin kuma da Sarkin Musulmi Muhammadu Bello, ya gina makarantu a kauyuka, sai ya aika da malam Musdafa Attorodi garin Salame domin karantarwa.Malam Musdafa Attorodi ya zauna a garin Salame har rasuwarsa, amma sai aka bisne shi a Wurno kusa ga sarkin Musulmi Muhammadu Bello.

Khadija ta yi sa’ar auren wannan babban malami, wanda ta ci gaba da karatu da neman ilimi a hannunsa.Zurfin ilimin da ta samu a gidansu da kuma gidan mijinta ya ba ta damar karantar da yara da manya fannonin Alkur’ani da Fikihu da Tauhidi da Hadisi da harshen Larabci da sauran fannonin ilimi.

Ta nakalci Alkur’ani da Tafsiri, domin a wakar Modibbo Kilo ta Hijira, ta fara da kawo Khadija a matsayin wadda ta fara yin Tafsiri ga mata.Ko da yake ba ta kawo sunan Khadija karara ba, amma ta ce babbar Diyar Usmanu kuma matar Tafa, don haka bincike ya gano cewa cikin ‘ya’yan Shehu, tana nufin Khadija.

Allah MaDaukakin Sarki Ya albarkaci Khadija da haihuwar Da Abdulkadir, wanda ya zama babban malami wanda ya auri Khadija (Khadijatus sugra) Diyar Sarkin Musulmi Muhammadu Bello.

Ayyukanta:

Ta yi rubuce-rubuce cikin harshen Fulatanci da Larabci da Hausa.Rubuce-rubucenta sun kunshi:

i. Wakoki a kan Fikihu da nahawun Larabci

ii. Marsiyya wadda ta rubuta game da rasuwar mijinta.

iii. Fassarar sanannen littafin nan Mukhtasar al-Khalil na mazhabar Maliki, fitaccen aikinta wanda ta wake a cikin harshen Fulatanci.

ib. Littafin Nahwu mai suna Katarunnada

Baya ga wadannan sanannun ayyuka na Khadija, bincike na ya sami gane waDansu wakokinta kamar haka:

Wakar Addu’a Game da Neman Nasarar Yaki

Wakar Ta’aziyya

WakarZuwan Mahdi

Wakar Godiya

Wakar Marsiyyar Mariyatu

Wakar GargaDi

Wakar Hanyar Shiriya

An ciro wannan bayanin ne daga mashahurin littafin nan da ya kunshi shi sahihin tarihin malamai mata da aka yi a lokacin jihadi da kafin jihadi da bayan jihadi, wanda Farfesa Sa’adiyya Omar ta wallafa. Marubuciyar ta yi kokin yin bincike tare da rairayo Gaskiya wajen binciken. Allah ya saka mata da alheri. Farfesa Sa’adiyya malama ce a cibiyar Nazarin Hausa Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto.

Exit mobile version