Bello Hamza" />

Kisan Hauwa Liman Ya Nuna Gazawar Gwamnatin Buhari –Sowore

Kisan da ‘yan kungiyar Boko Haram ta yi wa ma’aikaciyar jinyar nan mai aiki da kungiyar Red Cross ta duniya, Malama Hauwa Liman ya kara fito da gazawa da rashin iya aiki na Shugaban Kkasa Muhammadu Buhari a kokarin tsare rayukan al’ummar Nijeriya a wannan lokacin.

Wannan bayanin ya fito ne a wata sanarwar da Misis Rachel Onamusi-Kpiasi, jami’ar watsa labarai na kungiyar yakin neman zaben Omoyele Sowore na jam’iyyar AAC a matsayin shugaban kasa Nijeriya a zaben 2019 dake tafe.

Sanarwa ta huma ci gaba cewa, daga dukkan alamu jam’iyyar APC ta shagaltu ne kawai da hada hadar neman sake dawowa a kan karagar mulki a halin yanzu fiye a lura da tsaron rayukan ‘yan Nijeriya gaba daya. Gwamnatin ta kawar da idon ta daga abin dake faruwa yayin da sojoiji ke cika aljihunsu da kudadn da aka ware don yaki da ‘yan ta’adda tare da kare rayukan ‘yan Nijeriya, haka kuma dakarun sojojinmu na rasa rayukansu a kullum saboda rashin kayan aikin da za su fuskanci ‘yan Boko Haram a fage fama.

Sanarwa ta kuma kara da cewa, a kullum ‘yan ta’adda na garkuwa da ‘yan Nijeriya tare da karbar makudan kudade daga hannunsu a matsayin kudin fansa, ana kuma ci gaba da bautar da mata da yara kuma har yanzu babu wani magana daga bakin gwamnatin dake neman a sake zaben ta a karo na biyu. Amma gashi kusan awa fiye 24 da kashe Hauwa Liman har yanzu babu kalaman ta’aziyya zuwa ga iyalanta da nufin kwantar musu da hankali, tabbas gwamnatin da bata damu da yaruwar ‘yan kasarta ba bai kamata ta sake neman zabe a karo na biyu ba,” inji ta.

Ta kuma kara da cewa,”Ya kamata mu bayyana cewa, dan takarar shugabacin kasar nan da  jam’iyyar PDP ta tsayar, Atiku Abubakar ba zai iya kawo wa kasar nan canjin da take tsananin bukata ba, saboda haka lokaci ya yi da al’ummar kasar nan za su mayar da hankalinsu ga jagora matashi wanda za iya kawo kasar nan canjin da ya kamata tare da kawo wa kasar tsaron dukiya da rayukan ‘yan kasa, wannan kuma shi ne dan takarar shugabacin kasar nan na Sowore 2019,”

Daga nan ta yi addu’ar Allah ya jikan Hauwa Liman da Saifura Husseini Ahmed da kuma sauran dimbin ‘yan Nijeriya da suka halaka sakamakon sakacin gwamnati a kowanne mataki.

Exit mobile version