Babban sufeton ‘yansandan Nijeriya, Usman Baba, ya gana da gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, a hedikwatar rundunar da ke Abuja, inda suka tattauna, kan hanyoyin da za a bi domin yi wa lauyar da wani jami’in dan sanda ya kashe a Legas.
LEADERSHIP ta rawaito cewar gwamnan Jihar Legas ya yi alkawarin bai wa ‘yansanda goyon baya wajen ganin an yi adalci a cikin shari’o’in da ke kass kuma hada kai da ‘yan sanda kan shirye-shiryen bayar da shawarwari don ilimantar da ‘yan kasa kan fahimta da mutunta dokokin kasar don kyautata alaka da su.
- Sin Ta Fadada Samar Da Kwayoyin Ibuprofen Da Paracetamol
- An Gurfanar Da Matashi A Kotu Sakamakon Lakadawa Dan Sanda Dukan Kawo Wuka
Ya kuma bayyana cewa, gwamnatinsa za ta hada kai da ‘yansanda domin gudanar da kwasa-kwasai, horaswa da sauran hanyoyin tantance jami’an ‘yansanda a kowane fanni na aikin dan sanda.
Hakazalika Gwamna Sanwo-Olu ya jaddada bukatar samar da wasu kayan aiki kamar na’urorin daukar hoto na jiki, makamai, da dai sauransu, don dakile yawan amfani da iko da inganta aikin ‘yansanda.
A halin da ake ciki, Sufeton’yansandan yayin da yake mika ta’aziyyarsa ga iyalai da kuma ‘yan uwan mamaciyar, ya tabbatar da cewa za a bi diddigin lamarin har sai an yin adalci.
Kakakin ‘yansandan, CSP Olumuyiwa Adejobi, ya ce Sufeton ya kuma bayyana cewa rundunar tana aiki tare da babban mai shari’a na Jihar Legas domin tabbatar da cewa an gurfanar da mai laifin a gaban kotu da ke da hurumin yin shari’a domin zama izina ga wasu.
Sufeto-Janar na ‘yansandan ya kuma bukaci dukkan jami’an da su kiyaye mutunta doka da kuma hakkin kowa, wanda shi ne babban jigon aikin ‘yansanda duk da cewa ya bukaci jama’a da suke bai wa jami’an ‘yansanda hadin kai.