Koriya ta Arewa ta harba abin da ake zargi makami ne mai linzami ya wuce ta sararin saman Japan, wanda ya yi tafiyar kusan kilomitta 500 kafin ya fada Tekun Pacific.
Dama Koriya ta Arewa ta jima tana gwajin makamai masu linzami a shirinta na mallakar muggan makamai, to amma wannan shi ne na farko da ta harba ya bi ta samaniyar Japan tun 2017.
Ga abin da muka sani game da karfin kasar a fannin makami mai linzami.
Wadanne makamai masu linzami Koriya ta Arewa ke gwaji?
Koriya ta Arewa ta yi gwajin makamai masu linzami sama da 30 a shekarar nan, inda wasu daga cikinsu suke da karfin da za su iya cin dogon zangon da ya kai har Amurka.
Daya daga cikin makaman yana da sauri kamar na sauti kuma a kasa-kasa ta yadda na’urar gano makamai ba za ta iya ganinsa ba.
Ana ganin makamin da ta gwada kwanan nan, wanda ya bi ta saman Japan yana iya cin zangon da ya kai nisan kilomita 4,500 – nisan da zai iya kai wa har tsibirin Guam na Amurka.
Haka kuma Koriya ta Arewar na gwajin makami mai linzami samfurin Hwasong-14, wanda ke iya cin nisan zangon kilomita 8,000. Koda yake wasu nazarce-nazarcen na nuni da cewa zai iya cin nisan har kilomita 10,000, abin da hakan ke nufin zai iya kai wa har New York idan aka harba shi daga Koriya ta Arewa.
Wannan ne makami mai linzami na kasar na farko wanda zai iya tafiya daga wata nahiya zuwa wata nahiya.
Ana ganin makami mai linzamin da kasar ta kera tare da gwajinsa kwanan nan, mai suna Hwasong-15 yana iya tafiyar nisan kilomita 13,000, wanda hakan ke nufin zai iya kai wa dukkanin fadin kasar Amurka.
A watan Oktoba na 2020, Koriya ta Arewa ta bayyana makaminta mai linzami na baya-bayan nan mai suna Hwasong-17.
Shi kuwa ana ganin zai iya cin dogon zangon da ya kai kilomita 15,000 ko fi.
Zai kuma iya daukar dunkulen makami har guda uku ko hudu, a lokaci daya maimakon daya kawai, wanda hakan zai sa abu ne mai wuya wata kasa ta iya kare kanta daga makamin.
Kwararru sun ce kaddamar da sabbin makaman masu linzami da Koriya ta Arewa ke yi nuni ne ga gwamnatin Biden ta Amurka na irin karfin da kasar ke ci gaba da samu na soji.
A watan Maris na 2021, ta yi gwajin na’ura mai linzami da za ta iya dako da harba makami mai nauyin tan biyu da rabi, wanda hakan ke nufin zai iya daukar makamin nukiliya kenan.
Masu nazari a cibiyar hana bazuwar makaman nukuliya ta ‘James Martin Center for Nonproliferation Studies,’ sun sheda wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa wannan makami kusan sabon samfuri ne da aka inganta na KN-23 wanda kasar ta taba gwada wa a baya.
Wadanne makaman nukiliya kasar ta mallaka?
Lokaci na karshe da Koriya ta Arewa ta yi gwajin wani bam na nukiliya shi ne a 2017.
Fashewar da aka gani a wurin gwajin makamanta na Punggye-ri ta kai karfin kiloton 100-370.
Bam mai nauyin kiloton 100 ya ninka wanda Amurka ta jefa a birnin Hiroshima a 1945 ninki shida.
Koriya ta Arewa ta yi ikirarin cewa wannan shi ne bam dinta na nukiliya na farko, wanda shi ne mafi karfi a tsakanin dukkanin makaman nukiliya.
Sai dai kuma watakila kasar za ta yi kokarin gwajin wasu kananan makaman na nukiliya da ba su kai wancan karfi ba, in ji kwararre a cibiyar nazarin makamai ta Royal United Serbices Institute, Joseph Byrne.
A ina za ta iya gwajin makaman nukiliya?
Kasar ta yi gwajin makaman nukiliya a karkashin kasa sau shida a wurin gwajinta na Punggye-ri. Sai dai a 2018 Koriya ta Arewa ta ce za ta rufe wurin, saboda ta yi gwajin karfinta na nukiliya. Hukumomin Kasar ta Koriya ta Arewa sun gayyaci ‘yan jarida na waje inda suka lalata wurin a gabansu.
Sai dai abin da ba a sani ba shi ne ko kasar ta lalata wurin yadda ba za a iya sake amfani da shi ba ko kuma ba ta yi hakan ba.
Wasu hotunan tauraron dan-Adam da aka fito da su a shekarar nan sun nuna alamun cewa ana sake gyara wurin. Duk wani gwaji da za a yi a wurin zai saba yarjejeniyar kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.
Farfado da cibiyar hada makamanta na nukiliya
A shekara ta 2018, shugaban Koriya ta Arewar Kim Jong-un ya yi wa shugaban Amurka na lokacin Donald Trump alkawarin cewa, zai lalata dukkanin cibiyoyin kasarsa na hada makaman nukiliya.
Sai dai hukumar nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce wasu hotunan tauraron dan-‘Adam sun nuna alamun cewa, kasar ta sake farfado da cibiyarta ta hadawa tare da inganta sinadarin hada makamin nukiliya.
Mun ciro daga BBC HAUSA