Mai horar da ‘yan wasan kungiyar Barcelona, Ronald Koeman ya caccaki ‘yan wasansa sakamakon sakaci da suka yi a wasan da Cadiz suka lallasa su daci 2-1, ya na mai bayyana rashin jin dadinsa ganin yadda masu jan ragamar gasar La Liga, Atletico Madrid su ka ba su ratar maki 12 a halin yanzu.
Albaro Negredo ne ya ci kwallon da ta ba Cadiz nasara, bayan da ‘yan wasan Barcelona suka yi ta tafka kurakurai, har sai da mai tsaron raga Marc-Andre ter Stegen ya mika wa dan wasan gaban na Cadiz kwallo, shi kuwa ya antaya ta a raga.
Koeman ya ce kurakurai da bai kamaci tawaga irin tasa ba ne ummul’abaisan rashin nasarar da suka samu, kuma bai yi tsammanin irin wannan rashin kokari daga ‘yan wasansa ba saboda haka dole a kawo gyara.
Koeman ya ce hakan na nuni da cewa ‘yan wasansa ba su mayar da hankali a fafatawar ba, yana mai bayyana takaicinsa a game da rashin nasarar wadda tasa kungiyar har yanzu bata cikin kungiyoyin da za su iya lashe gasar La ligar bana.
Yanzu wasa na gaba shine wanda Barcelona zata karbi bakuncin kungiyar kwallon kafa ta Jubentus a yau a wasan karshe na cikin rukuni a gasar cin kofin zakarun turai kuma duk kungiyar data samu nasara itace za tayi ta daya a cikin rukunin nasu.