Tawagar mata ’yan ƙasa da shekaru 17 ta Koriya ta Kudu ta fara gasar cin kofin duniya ta wannan rukuni da ƙafar dama, bayan ta lallasa Puerto Rico da ci 6-0 a wasansu na farko na Rukunin B da aka buga a Rabat, ƙasar Morocco.
Rukunin B ya ƙunshi ƙasashe huɗu, wato Najeriya, Koriya ta Kudu, Puerto Rico da Poland.
Wannan nasara ta sa Koriya ta Kudu ta hau saman teburin rukunin da maki uku, yayin da Puerto Rico ta koma matakin ƙarshe.
A wani wasan kuma, Jamus ta doke Argentina da ci 2-1 a karawar da suka yi a Rukunin A.
A halin yanzu, tawagar Najeriya za ta kara da Poland da ƙarfe 7 na dare agogon Nijeriya.
’Yan wasan Nijeriya na fatan fara gasar da nasara, yayin da suke ƙoƙarin lashe kofin duniya a wannan karon.














