Da safiyar yau Asabar, firaministan kasar Sin Li Qiang, ya halarta tare da gabatar da jawabi a bikin bude taron kasa da kasa na 2026 kan likitancin gargajiya a birnin Beijing.
Li Qiang ya ce likitancin gargajiya na zaman wani karfi na musammam da ke kare lafiyar dan adam da bunkasa nasarar wayewar kai. Ya ce la’akari da shafe lokaci mai tsawo ana amfani da shi, likitancin gargajiya na Sin ya samar da wata hanya ta musammam ta samun ci gaba.
Ya ce ya kamata kasashen duniya su karfafa hadin gwiwa da kuma amfani da albarkatun likatancin gargajiya na duniya da hada shi cikin tsarin kiwon lafiya, da aiki tare domin shawo kan kalubalen lafiya da dan adam ke fuskanta.
A cewar firaministan, kasar Sin za ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta iya karfinta da bayar da gudunmuwa wajen cike gibin kiwon lafiya da ake da shi a duniya. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)














