- Ma’aikatan Jihar Za Su Rika Aiki Daga Gida
Daga Khalid Idris Doya,
Bisa barkewar annobar Korona karo na biyu, Gwamnatin Jihar Kwara a jiya Laraba ta kulle jihar, amma kulle wanda ba mai tsanani ba, domin kare jama’an jihar daga yaduwar cutar.
Mataimakin Shugaban kwamitin yaki da korona a jihar, Razak Raji ya shaida wa ‘yan jarida a Illorin cewa amfani da takunkumin rufe hanci da baki a cikin jama’a ya zama dole a fadin jihar, inda ya kara da cewa dukkanin wani tarukan jama’a da bukukuwan da ke haifar da cunkoson jama’a an dakatar da shi har zuwa nan da wani lokaci.
“Wuraren ibada ba a amince musu su hadu a lokaci guda sama da kashi 50 na girman wajensu ba. Wannan zai bada dama a samu bada tazara da kiyaye ka’idar rage cinkoson jama’a.
“Dukkanin wani taron da zai hada mutum sama da 50 ba a amince da yin sa ba. Sannan wurare su sanya matakin in babu takunkumin rufe fuska da hanci to kada su bar mutum ya shiga.”
Raji, wanda kuma shine kwamishinan lafiya na jihar, ya kara da cewa, “Ma’aikata an umarce su da suke gudanar da ayyukansu daga gida. Ma’aikatan da ke bakunan ayyukan musamman ne kawai aka amince su cigaba da gudanar da ayyukansu yadda suka saba musamman ma’aikatan lafiya. Ganawa ta bidiyo shine abun da ya fi dacewa a yanzu.”
“A bangaren sufuri, an bada umarnin dole direbobi da fasinjoji da su ke amfani da kyallen rufe hanci da baki. Akwai hukunci da ladaftarwa ga dukkanin wadanda suka karya dokokin da aka sanya.
“An samar da jami’an tsaron da za su tabbatar an bi dokoki da ka’idojin da aka sanya domin tabbatar da jama’a sun bi matakan kariya. Wadanda suka karya dokar da aka sanya su na barazana wa lafiyar jama’a.”