Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke hukunci kan hana Gwamnatin Tarayya tsoma baki a kuɗaɗen ƙananan hukumomi 44 na jihar. Mai shari’a Musa Ibrahim Ƙaraye ne ya yanke wannan hukunci a ranar Litinin, bayan ƙarar da wakilan ƙananan hukumomi suka shigar don kare ‘yancin cin gashin kansu na kuɗi.
Shari’ar ta samo asali ne bayan da jam’iyyar adawa ta APC ta bukaci kotu da ta dakatar da sakin kuɗaɗen ƙananan hukumomi, bisa zargin cewa an yi maguɗi a zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a watan Oktoba 2024. Hon. Abdullahi Abbas, Hon. Aminu Aliyu Tiga, da jam’iyyar APC ne suka jagoranci shigar da ƙarar, inda suka tuhumi CBN, da FAAC, da ƙananan hukumomi 44 a gaban kotu.
- An Kaddamar Da Cibiyar Ilimin Fasahar Zamani Ta Sin Da Afirka A Jami’ar Kenya
- Gwamnan Kano Ya Gargaɗi Malamai Kan Sa Yara Aikin Wahala
Duk da haka, kotun ta yanke hukunci a ƙananan hukumomin Kano, inda ta haramta wa Gwamnatin Tarayya da hukumominta tsoma baki ko tsaida kuɗaɗensu. Lauyan ƙananan hukumomi 44, Barrister Bashir Wuzirchi, ya bayyana hukuncin a matsayin nasara ga jihar Kano.
“Mun shigar da wannan ƙara ne don hana wasu ɓoyayyun hannaye hana ci gaban Kano ta hanyar dakatar da kuɗaɗen ƙananan hukumomi. Alhamdulillah, yau kotu ta ba mu nasara kuma ta umarci Gwamnatin Tarayya da ta daina tsoma baki a waɗannan kuɗaɗe da doka ta amince da su,”
in ji shi.
Sai dai kakakin APC a Kano, Ahmad Aruwan, ya bayyana cewa jam’iyyar za ta ɗaukaka ƙara.
“Hakkinmu ne mu tabbatar da cewa kuɗin jama’a ba su faɗa hannun jagorori marasa cancanta ba. Saboda haka, za mu ɗaukaka ƙara kuma mu ci gaba da fafutuka har sai an yi mana adalci,”
in ji shi.