• English
  • Business News
Thursday, May 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ku Yi Amanna Da Tinubu, Matsalolin Zu Su Zo Karshe, inji Ministan Yaɗa Labarai

by Sulaiman
1 year ago
in Labarai
0
Ku Yi Amanna Da Tinubu, Matsalolin Zu Su Zo Karshe, inji Ministan Yaɗa Labarai
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris Malagi, ya roƙi ‘yan Nijeriya da su yi haƙuri su yi imani da gwamnatin Tinubu.

Idris ya yi wannan kiran ne a ranar Laraba yayin buɗa baki da ya yi tare da shugabanni da ma’aikatan kafafen yaɗa labarai wanda ma’aikatar ta shirya a ɗakin taro na Armani Events Centre da ke Kano.

  • Gwamnatin Jihar Yobe Ta Kashe N2.9bn Wajen Sayen Takin Zamani —kwamishina
  • Zanga-zangar Minna: Shugaba Tinubu Ya Ba Da Umarnin A Sassauta Farashin Kayan Abinci – Idris

Idris ya ce gwamnatin Tinubu tana aiki tuƙuru domin ganin ta shawo kan matsalar tattalin arziƙin ƙasar nan.

Ya ce, “Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai ta himmatu wajen tabbatar da gyaran hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatar da nufin inganta fannin.”

Ministan ya ƙara da cewa gwamnatin na ƙoƙarin farfaɗo da matatun man fetur na ƙasar nan, inda ya bayyana cewa nan ba da daɗewa ba matatar mai ta Fatakwal za ta fara aiki.

Labarai Masu Nasaba

Majalisar Wakilai Za Ta Binciki Yadda Aka Samu Mummunan Sakamakon Jarabawar UTME 2025

HOTO: Ofishin Tsohon Shugaban Kasa Shagari Bayan Shekara 42

Game da cire tallafin man fetur da aka yi, Idris ya ce Nijeriya ta fuskanci raguwar yawan man da ake amfani da shi a cikin gida na kimanin lita biliyan ɗaya bayan cire tallafin, wanda ya nuna kashi 53 cikin 100 na yawan man da ake amfani da shi da farko.

Ya ƙara da cewa, “Hakan ya bayyana yadda ake safarar man fetur ɗin mu ta kan iyakokin ƙasar nan domin amfanar waɗanda ba sa biyan ƙasar nan haraji”.

Ya jaddada cewa cire tallafin man fetur ya zama dole domin waɗanda ba sa biyan haraji sun fi ‘yan Nijeriya cin gajiyar tallafin.

A cewar sa, “Abin da ake amfani da shi na man fetur a cikin gida ya ragu da kusan kashi 53 cikin 100, ma’ana sama da lita biliyan ɗaya da muke amfani da ita a lokacin cire tallafin ta ƙare a yanzu. Kuma tambayar da za ku yi wa kan ku ita ce: Ina wannan man ya ke zuwa?

“Yaya ba zato ba tsammani amfanin cikin gida ya ragu da kashi 53 cikin 100? Wannan yana nufin cewa wannan man fetur ɗin ya samo hanyar fita daga kan iyakokin mu don amfanin waɗanda ba sa biyan haraji ga ƙasar nan.

“Ba shi da ma’ana a ci gaba da ba wa gidan wani tallafi lokacin da rufin ku ke ɗiga, taga ta karye, kuma yaron ku bai je makaranta ba. Dole ne ku tallafa wa kan ku kafin ku ba wa wani tallafi.”

A kan abin da gwamnati ke yi don rage wahalhalun da ke tattare da cire tallafin, sai ya ce, “Akwai ƙarin albashi na wucin gadi na naira 35,000 a kowane wata na wata shida – an riga an biya na watanni huɗu.

“Gwamnonin Legas, Osun, Oyo, Ogun, Jigawa, Adamawa, Ebonyi, Neja, Ondo da Ekiti su ma sun ɗauki wannan shiri na Gwamnatin Tarayya na biyan albashin ma’aikatan su. An buƙaci sauran gwamnatocin jihohi su aiwatar da irin wannan.

“An kafa Kwamiti Uku kan sabon mafi ƙarancin albashi kuma tuni ya fara aiki. Masu ruwa da tsaki a shiyyar siyasa guda shida su na gabatar da takardar da ke nuna sabon mafi ƙarancin albashi ga gwamnati, ana ci gaba da tattarawa.

“Shugaba Tinubu ya amince da kafa Asusun Tallafawa Ababen More Rayuwa ga Jihohi don su zuba jari a muhimman wurare da za su samar da yanayi mai kyau ga ‘yan kasuwa kuma akwai shirin fitar da motoci masu amfani da gas na naira biliyan 100, don isar da motocin bas masu amfani da gas, da kayan aikin canza motocin.

“Tuni, Shirin Shugaban Ƙasa na Iskar Gas (CNG) ya fara tallafa wa abokan hulɗa masu zaman kan su da na gwamnati a wannan fanni.

“An fara bayar da kuɗi naira 25,000 a kowane wata ga miliyan 15 daga cikin gidaje mafiya talauci da marasa galihu a Nijeriya, wanda aka shirya na tsawon watanni uku. Magidanta 3,140,819 sun riga sun sami biyan kuɗi na farko kafin a dakatar da shirin don dubawa da gyarawa.

“Shugaba Tinubu ya kuma bayar da umarnin a fitar da hatsi tan 42,000 daga Asusun Ajiya na Nijeriya, don raba wa marasa galihu kyauta da Jami’an Tsaron Farin Kaya (DSS) da Hukumar Ba Da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) suka himmatu wajen sa ido a kan rarrabawar.

“Shugaban ya kuma amince da naira biliyan 100 don tallafa wa Asusun Raya Aikin Noma na Ƙasa (NADF) a shekarar 2024 kuma Ma’aikatar ta fara aiwatar da ayyukan fitar da naira biliyan 200, wanda Shugaban Ƙasa ya amince da shi, ta hanyar sababbin kuɗaɗen shiga tsakani na musamman guda uku wanda aka kafa a matsayin wani ɓangare na matakan kawo sauƙin kawar da tallafin ga ‘yan kasuwa, waɗanda su ne: Shirin Bayar da Tallafin Kuɗi na Shugaban Ƙasa (PCGS), Asusun Tallafawa na FGN MSME, da Asusun Fannin Masana’antu na Gwamnatin Tarayya.”

Ministan ya ƙara da cewa a wani yunƙuri na sauƙaƙa shiga shirin lamuni na ɗalibai, da magance ƙalubalen da ake fuskanta da kuma inganta yadda ake aiwatar da shi, Shugaba Tinubu ya rubuta wa Majalisar Dattijai takarda inda ya buƙaci a soke da kuma sake kafa dokar lamuni ta ɗalibai.

Daga nan sai ya yi alƙawarin cewa Shirin Zuba Jari na Jama’a zai dawo da ƙwarin gwiwa bayan an yi nazari sosai kan yadda ake tafiyar da shi, inda ‘yan Nijeriya da suka kammala karatun su a matakin gaba da Bautar Ƙasa (NYSC), da masu riƙe da OND za a riƙa biyan su alawus-alawus na wata-wata, ta hanyar Shirin Bayar da Lamuni na Jama’a har sai sun samu ayyukan yi.

Ya kuma ce shugabannin Babban Bankin Nijeriya (CBN) da suka shuɗe ba su tafiyar da babban bankin yadda ya dace ba, amma Tinubu ya dawo da martabar babban bankin da ya ɓata.

“Ajandar Sabunta Fata ta Shugaban Ƙasa ta fara samar da sakamako mai kyau, saboda tattalin arziƙin ƙasar yana farfaɗowa sannu a hankali, kuma matsalolin za su ƙare,” inji shi.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Gwamnatin TinubuTabarbarewar Tattalin ArzikiTsadar Rayuwa
ShareTweetSendShare
Previous Post

Gwamnan Bauchi Ya Yi Wa Fursunoni 96 Afuwa, Ya Bai Wa Kowa Kyautar Dubu 100

Next Post

Tinubu, Ka Taka Wa Wike Birki Ko Ka Fadi Warwas A Abuja A 2027 – Shugabannin APC

Related

Majalisa Ta Yi Watsi Da Ƙudirin Dokar Karɓa-karɓa A Kujerar Shugaban Ƙasa A Tsakanin Shiyyoyin Nijeriya
Labarai

Majalisar Wakilai Za Ta Binciki Yadda Aka Samu Mummunan Sakamakon Jarabawar UTME 2025

23 minutes ago
HOTO: Ofishin Tsohon Shugaban Kasa Shagari Bayan Shekara 42
Labarai

HOTO: Ofishin Tsohon Shugaban Kasa Shagari Bayan Shekara 42

2 hours ago
‘Yan Bindiga Sun Sace Sarki Mai Daraja Ta Ɗaya A Kogi
Manyan Labarai

‘Yan Bindiga Sun Sace Sarki Mai Daraja Ta Ɗaya A Kogi

4 hours ago
An Bayar Da ₦95m Ga Iyalan Maharba Da Mutanen Da ‘Yan Ta’adda Suka Kashe A Bauchi
Labarai

An Bayar Da ₦95m Ga Iyalan Maharba Da Mutanen Da ‘Yan Ta’adda Suka Kashe A Bauchi

6 hours ago
Lassa Da Shawara Sun Kashe Mutum 183 A Jihohi 36 Da Abuja
Labarai

Lassa: Mutane 138 Sun Rasu, 717 Sun Kamu A Jihohi 18 – NCDC

9 hours ago
Wa Suka Fi Cancanta A Nada Ministocin Tinubu?
Da ɗumi-ɗuminsa

Tinubu Ya Ƙaddamar Da Dakarun Da Za Suke Tsaron Daji Don Yaƙar ‘Yan Ta’adda

10 hours ago
Next Post
Babu Wani Shiri Na Kwaso ‘Yan Nijeriya Daga Falasdin Ko Isra’ila –Gwamnatin Tarayya

Tinubu, Ka Taka Wa Wike Birki Ko Ka Fadi Warwas A Abuja A 2027 - Shugabannin APC

LABARAI MASU NASABA

Majalisa Ta Yi Watsi Da Ƙudirin Dokar Karɓa-karɓa A Kujerar Shugaban Ƙasa A Tsakanin Shiyyoyin Nijeriya

Majalisar Wakilai Za Ta Binciki Yadda Aka Samu Mummunan Sakamakon Jarabawar UTME 2025

May 15, 2025
Ma’aikatar Kasuwanci Ta Sin Ta Yi Karin Haske Kan Huldar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka

Ma’aikatar Kasuwanci Ta Sin Ta Yi Karin Haske Kan Huldar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka

May 15, 2025
An Kaddamar Da Yankin Gwajin Aikin Gona Da Sin Ta Gina A Zimbabwe

An Kaddamar Da Yankin Gwajin Aikin Gona Da Sin Ta Gina A Zimbabwe

May 15, 2025
HOTO: Ofishin Tsohon Shugaban Kasa Shagari Bayan Shekara 42

HOTO: Ofishin Tsohon Shugaban Kasa Shagari Bayan Shekara 42

May 15, 2025
Shawarwarin Raya Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka Sun Haifar Da Managarcin Sakamako

Shawarwarin Raya Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka Sun Haifar Da Managarcin Sakamako

May 15, 2025
‘Yan Bindiga Sun Sace Sarki Mai Daraja Ta Ɗaya A Kogi

‘Yan Bindiga Sun Sace Sarki Mai Daraja Ta Ɗaya A Kogi

May 15, 2025
Shugaba Xi Ya Amsa Wasikar Da Jagoran Da Ya Kafa Majalisar Cinikayya Ta Denmark A Sin Ya Aike Masa

Shugaba Xi Ya Amsa Wasikar Da Jagoran Da Ya Kafa Majalisar Cinikayya Ta Denmark A Sin Ya Aike Masa

May 15, 2025
An Bayar Da ₦95m Ga Iyalan Maharba Da Mutanen Da ‘Yan Ta’adda Suka Kashe A Bauchi

An Bayar Da ₦95m Ga Iyalan Maharba Da Mutanen Da ‘Yan Ta’adda Suka Kashe A Bauchi

May 15, 2025
NNPP Ta Tafka Asara, Ƴan Majalisa 2 Daga Kano Sun Koma APC

NNPP Ta Tafka Asara, Ƴan Majalisa 2 Daga Kano Sun Koma APC

May 15, 2025
Ya Kamata A Kori Ministan Ilimi – Aisha Yesufu

Ya Kamata A Kori Ministan Ilimi – Aisha Yesufu

May 15, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.