Hussain Sulaiman" />

Kungiyar FOMWAN Ta Jihar Kano Ta Raba Kayan Tallafi Ga Marayu

Kwanakin baya ne kungiyar mata musulmi FOMWAN ta jihar Kano karkashin shugabancin Malama Sa’adatu Hashim, ta raba kayan tallafin abinci ga shugabannin kungiyar dake kana nan hukumomin jihar 44 inda za su raba su ga marayun dake karkashin kulawar su.
Malama Sa’adatu Hashim ta shaida wa manema labarai a lokacin rabon tallafin cewa kayayyakin da suka raba sun hada da buhunnan Shinkafa 12 buhunan Siga 12 dilar gwanjo 12 katan na Taliya 12.
Malam Sa’adatu ta ce sun samu wannan kayayyakin ne daga hukumar kwastan ta jihar Kano, saboda haka ta nuna farin cikin ta da wannan kayan tallafi da suka samu domin raba wa marayun na jihar Kano. Shugabar ta Fomwan ko bayan tallafin da suka samu daga hukumar kwastan kungiyar su duk shekara suka raba kayayyakin abinci ga marayu tare da sauran mabukata,suna kuma saran da yardar Allah za su raba kayan tallafin nan ba da jimawa ba.
Sai dai ta jawo hankalin kwasatan idan za ta sake raba kayan nan gaba ta tuna cewa suna da kungiyoyin marayu masu yawa a jihar Kano kamata ya yi ta ribanya .
Ta jawo hankulan marayun da suka amfana da su yi amfani da kayan da suka samu ta hanyoyin da suka kamata ka da su sayar da shi a kasuwa.
Kungiyar su ta dauki kwararan matakai wajen ganin shugabannin kungiyar da ke kananan hukumomin jihar 44 sun raba kayan kamar yadda aka umurci da su yi . Ta kuma gode wa shugabannin kungiyar na kananan hukumomin jihar a bisa hadin kan da suke ba ta wajen tafiyar da shugabancin kungiyar a jihar Kano.

Exit mobile version